Zagayen kamfe: Janar Buhari ya yi alkawarin magance matsalolin kasar nan
dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammad Buhari mai ritaya, ya ce idan aka zabe shi zai magance matsalolin tsaro da cin hanci da rashawa da rashin aiki da lalacewar ilimi a kasar nan. Janar Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a Jos a […]
dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammad Buhari mai ritaya, ya ce idan aka zabe shi zai magance matsalolin tsaro da cin hanci da rashawa da rashin aiki da lalacewar ilimi a kasar nan.
Janar Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a Jos a ranar Asabar inda ya ce a shekara 16 da Jam’iyyar PDP ta yi tana mulkin kasar nan, harkokin da dama sun tabarbare. “Idan aka zabe mu, za mu magance abubuwan da suke faruwa a yankin Arewa maso Gabas, za mu samar wa matasa aikin yi ta hanyar rungumar noma da harkokin ma’adanai, kuma za mu tabbatar mun ba matasan kasar nan ilimi,” inji shi.
A wajen taro an karbi wasu gaggan’yan Jam’iyyar PDP a Jihar Filato da suka koma Jam’iyyar APC da suka hada da tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Jihar Misis Pauline Tallen da tsohon Shugaban Asusun Horar da Ma’aikata na kasa (ITF) Farfesa Sambo Wapmuk da sauransu.
A lokacin taron komai ya tsaya cik a garin Jos, saboda yadda dubban magoya bayan Janar Buhari Musulmi da Kirista suka fito don tarbarsa.
A Jihar Nasarawa dimbin magoya bayan Jam’iyyar APC sun yi cikar kwari a Dandalin Taro na Lafiya domin marabar da Janar Muhammadu Buhari wanda yana isowa ya kaddamar da babban filin taron na miliyoyin Naira da gwamnatin Umaru Tanko Al-Makura ta gina.
Janar Buhari, ya jinjina wa magoya bayansa kuma ya ce idan har aka zabe shi zai mayar da hankali ne wajen raya ilimi da kiwon lafiya da noma da harkokin ma’adinai da sauransu inda ya ce hakan zai taimaka wa talakan Najeriya.
Ya nuna rashin jin dadinsa kan da yadda al’amuran tsaro da sauransu suka tabarbare a kasar nan inda ya yi alkawarin kawo karshensu.
A jawaban Farfesa Yemi Osibanjo da shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Mista Philips Tatari Sheku da Sanata Abdullahi Adamu da sauransu sun bayyana bukatar samun canji ne a kasar nan don gyara abubuwan da suka lalace.
Gwamna Umaru Tanko Al-Makura bayan ya karbi tutar jam’iyyar ya yi alkawari idan al’ummar jihar suka sake zabensa gwamnatinsa za ta karfafa bin doka da oda da tabbatar da zaman lafiya a jihar baki daya.
A ya yin taron an karbi wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka canja sheka zuwa APC da suka hada da Sanata John danboyi da Daraktan Yakin Zaben dan Takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyyar PDP da sauransu.
A Kaduna Janar Muhammadu Buhari ya ce zai gyara tattalin arzikin kasar nan a cikin shekara kuma ya kuma ce zai mayar da hankali ga batun tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da inganta tattalibn arziki idan aka zabe shi a watan gobe.
“Ba zan fada muku wasu sababbin abubuwa ba, illa batutuwa uku; tsaro da tattalin arziki da yaki da rashawa. Idan babu tsaro ta yaya jama’a za su yi sana’oinsu har su ciyar da iyalinsu. Gwamnatin PDP ta lalata kasar nan a cikin shekara 16 na mulkinta kuma abin da muka fito canjawa ke nan. Idan kuka zabi APC, ba wani kuka taimakawa ba illa kanku.”
Ya ce abin bakin ciki shi ne Jihar Kaduna wadda cibiya ce ta masana’antu a Arewa yanzu duk sun ruguje, masaku da fannin jirgin sama da sauran kamfanoni duk sun ruguje saboda rashin ingancin gwamnatin PDP.
Shugaban Jam’iyyar APC a yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir ya ce kwarai Buhari na fama da rashin lafiya, amma na bakin cikin cin hanci da rashawa da lalacewar hanyoyin motoci a kasa da cutar yin alkawari babu cikawa da kuma cutar rashin iya mulki da gwamnatin PDP ta yi suna a kai.