Zagi ta whatsapp ya haifar wa Balarabe hukuncin kora daga qasa da tara
Kotun daukaka kara ta Sharjah a Hadaddiyar Daular Larabawa ta samu wani Balarabe da laifin aikewa da sakon batanci da zage-zage ga matarsa, ta kafar sadarwa ta Whatskpp, don haka aka ci tarasa dirham dubu 10, wato daidai da Naira dubu 800, sannan za a fitar da shi daga kasar, kamar yadda lauyan mai laifin […]
Kotun daukaka kara ta Sharjah a Hadaddiyar Daular Larabawa ta samu wani Balarabe da laifin aikewa da sakon batanci da zage-zage ga matarsa, ta kafar sadarwa ta Whatskpp, don haka aka ci tarasa dirham dubu 10, wato daidai da Naira dubu 800, sannan za a fitar da shi daga kasar, kamar yadda lauyan mai laifin ya bayyana wa jaridar Gulf news. |
Kuma alkali Obaid Mohammad Ebrahim Mubarak ya yanke masa hukuncin ne duk da kasancewar shi ba ya nan.
Ma’auratan sun yi cacar baki ne har ta kai ga mijin ya bar gidan. Daga nan sai ya aike mata da sakon munanan kalamai ta whatsapp. Ita kuwa sai ta kai kara wata kotu a Sharjah, inda take bin kadin hakkin zagin da mijinta ya yi mata ta Whatsapp.
“Ya aiko da sakon tes a Whatsapp cike da munanan kamalai,” inji ta.
Kotun farko da aka fara kai karar, sai ta umarci mijin da ya biya diyya dirham dubu bioyar, amma mai gabatar da kara ya ki amince da hukuncin, don haka ya daukaka kara. A karshe kotun daukaka kara ta Sharjah ta kara wa mijin hukuncin kora daga kasar bayan ya biya dirhami dubu biyar, wato daidai da Naira dubu 400 na tara. An hukunta mutumin bisa tanadin dokar yaki da miyagun laifuffuka da ake aikata ta kafafen sadarwar zamani.