Zagin Buhari: Fayose na kunyata zuriyarmu – Yayansa

Yayan Mista Ayo Fayose Gwamnan Jihar Ekiti, Segun Fayose, ya roki Gwamnan ya daina kunyata zuriyarsu. Segun Fayose ya ce mahaifinsu dattijon limamin Kirista ne da ya samar da kyakkyawan suna ga iyalansa kafin ya bar duniya.Yayan Gwamna Fayose ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wata kafar labarai a Ibadan, fadar Jihar […]

Zagin Buhari: Fayose na kunyata zuriyarmu – Yayansa
Zagin Buhari: Fayose na kunyata zuriyarmu – Yayansa

Yayan Mista Ayo Fayose Gwamnan Jihar Ekiti, Segun Fayose, ya roki Gwamnan ya daina kunyata zuriyarsu.

Segun Fayose ya ce mahaifinsu dattijon limamin Kirista ne da ya samar da kyakkyawan suna ga iyalansa kafin ya bar duniya.
Yayan Gwamna Fayose ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da wata kafar labarai a Ibadan, fadar Jihar Oyo.
Ya ce maimakon Gwamnan ya ci gaba da kare kyakkyawan sunan da ya gada, sai ya koma yana kunyata zuriyar gidan Fayose ta hanyar cin zarafin manyan mutane kamar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari.
Segun Fayose wanda akanta ne da ke zaune a Ingila, ya ce iyalansu na mutunta sunan da suka gada daga mahaifinsu. Ya ce mahaifinsu ya mutu yana mai sadaukar da kai, kuma an shaidi iyalansa a Ekiti da kyawawan dabi’u da ake samu a wurin duk wanda ya fito daga zuriyar Omoluabi.
Ya bayyana Cif Obasanjo a matsayin wanda ya nuna Ayo Fayose duniya ta san shi.
Segun ya ce: “Abin takaici ne yadda ’yan Najeriya suke girmama miyagun mutane. Ina bakin ciki kan yadda ’yan Najeriya suke zabar mutane irin su Ayodele (kanensa) a matsayin Gwamna. ’Ya’yana ba za su iya zuwa Najeriya ba, saboda mugun halin da ake ciki a kasarmu.”
Ya kara da cewa, “Ba na hulda da wani daga cikin shugabanninmu saboda miyagun ayyukansu, don haka duk wanda zai ce na karbi kudi daga ’yan adawa ya fito fili ya kalubalance ni. Ekiti da Najeriya sun fi sunan Fayose girma kuma dukkan sunayen wajibi ne a kare su.”
Ya ce: “Ba na bukatar komai daga kowa, amma akwai bukatar Ayo ya daina cin zarafi da bata sunan babanmu. Saboda halayen Fayose, mutane da dama sun dauka iyalan Fayose marasa tarbiyya ne, amma a gaskiya ba haka ba ne. Na sha yi masa magana, amma ya ki ji. Buhari da Obasanjo sun kai su zama iyayensa, don haka ban san me ya sa yake cin mutuncinsu ba.”
Segun Fayose ya ce: “Kullum ina bakin ciki da halin da kasar nan take ciki. Girman kan Ayo na daya daga cikin dalilan da suka sa na ce kada mutane su zabe shi kafin zaben Gwamnan Jihar Ekiti. Idan abin da nake fad aba gaskiya ba ne, ’ya’yana shida sum utu kuma kada karshena ya yi kyau.”
Yayan Gwamnan ya kara da cewa: “Galibin mu da ke waje ba mu jin dadin abin da ke faruwa a Najeriya. Muna cike da bakin ciki. Kuma a duk lokacin da mutane suka kira ni ta waya daga Ekiti suna korafi a kan Ayo, naka ce musu su yafe wa iyalanmu. Kada mutane su rika ganin Ayo a matsayin jakadan iyalanmu.”