Zai biya matarsa diyyar Naira miliyan 40 don harbinta da kanjamau

A ranar Larabar makon jiya ne Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi a birnin Kano ta umarci wani mutum da tsohuwar matarsa ta yi kararsa cewa ya harbe ta da cutar kanjamau cewa ya biya ta diyyar Naira miliyan 40. Matar mai suna A’isha Mansur ta shaida wa kotun cewa mijinta Mansur Musa ya […]

Zai biya matarsa diyyar Naira miliyan 40 don harbinta da kanjamau
Zai biya matarsa diyyar Naira miliyan 40 don harbinta da kanjamau

A ranar Larabar makon jiya ne Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi a birnin Kano ta umarci wani mutum da tsohuwar matarsa ta yi kararsa cewa ya harbe ta da cutar kanjamau cewa ya biya ta diyyar Naira miliyan 40.

Matar mai suna A’isha Mansur ta shaida wa kotun cewa mijinta Mansur Musa ya sa harbe ta da cutar kanjamau sannan ya sake ta, don haka take neman kotu da ta karba mata diyyar Naira miliyan 40 daga hannunsa a matsayin kudin da za ta rika neman magani.
Bayan sauraren shari’ar na tsawon lokaci tare da gamsuwa da shaidun da mai karar ta gabatar, kotun a karkashin Mai shari’a Malam Muhammad Rabi’u Dausayi ta umarci tsohon mijin ya biya ta kudin da ta nema.
Lauyar matar Barista dalhatu Shehu Usman, ya yi wa Aminiya karin haske game da shari’ar inda ya ce sun gode wa Allah kan wannan nasara da suka samu. Ya ce akalla hukuncin zai zama darasi ga masu tunanin aikata irin wannan laifi, “Saboda idan aka duba da niyya wannan mutum yake sanya wa matan da yake aure cutar. Tunda ya san cewa yana da ciwon bai kamata ya ci gab da aure-aure ba,” inji shi.
Game da yadda za su karbi diyyar, Barista dalhatu ya ce tunda kotu ta yanke hukuncin ya biya wannan kudi za su jira su ga ranar da zai kawo idan kuma har mako biyu ya cika bai biya ba za su je su sayar da gidansa na Abuja da Malumfashi su dauki kudinsu.
Duk kokarin Aminiya ta yi don jin ta bakin wanda aka yi kara ya ci tura haka shi ma lauyansa Aminu Sarki ya ce tuni ya zare hannunsa game da shari’ar saboda Alhaji Mansur din ba ya daukar shawara.
Idan za a iya tunawa fara sauraren shari’ar ce a Kotun Shari’a ta Lardi da ke Nomansland a karkashin mai shari’a Alkali Faruk Ahmed amma ba a cimma matsaya ba, inda a karshe alkalin kotun ya mayar da shari’ar zuwa Kotun Shari’ar Musulunci ta Lardi da ke Kasuwar Kurmi.
A’isha Mansur ta taba shaida wa Aminiya cewa kafin su yi aure da tsohon mijin nata lafiyarta lau, sai bayan an ta haihu da shi ne sannan ta san cewa ta kamu da cutar HIb. “Kasancewar ya san yana da cutar bayan mun yi aure na samu ciki da na nemi na rika zuwa asibiti domin awon ciki sai ya nuna cewa shi a gidansa ba a zuwa asibiti. Daga baya ne likitoci suka tabbatar min ina tare da cutar HIb suka nemi in kai mijina. Da muka je ne sai suka ce ai shi ya fi shekara goma yana karbar magani a wurinsu. Daga nan na komo gidanmu Kano na haihu daga baya aka mayar da ni gidansa a can Abuja ganin na riga na kamu da cutar babu kuma wani abu da za a iya yi a kai. A haka muka zauna da shi yau fari, gobe tsumma har zuwa ranar da muka yi rigima inda ya yi min duka tare da yanyanka ni a jiki,” inji ta.
Malama A’isha Mansur ta ce rigimarsu da mijinta ta samo asali ne a ranar da ya yi amarya, “Bayan amaryarsa mai suna A’isha Katsina ta tare a gidanmun na Malumfashi sai na shiga dakinta na gaya mata halin da mijinmu yake ciki. Na gaya mata cewa kada ta soma yarda ya kusance ta. Da farko ba ta gaskata ni ba domin a tunaninta kissa nake yi mata don kada ta zauna a gidan, har tana cewa wai me ya sa ni nake zaune a gidan. A nan ne na shaida mata cewa ni ma don na riga na kamu da cutar ne, amma da a ce
uwargidansa ta sanar da ni, to babu abin da zai sa na zauna a gidan,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa, “To bayan ango ya shiga dakin amarya sai ta ga duk ilahirin jikinsa a rame, ba yadda ta saba ganinsa a lokacin da yake zuwa zance gidansu ba, ashe sutura yake cikawa a jikinsa inda yake zama mai kiba. Nan take amarya ta yi tsalle gefe ta gaya masa cewa ba za ta zauna a gidan ba har sai sun je an yi musu gwajin cutar kanjamau. Nan take ya ce ya san babu wanda zai gaya wa amryarsa wannan magana sai ni, don haka ya taho dakina cikin sauri. Kwatsam, sai jin saukar duka a kaina, ya yi min dukan kawo
wuka har da dauko wuka ya yanyanke ni a fuska da kirji da hannayena, kuma ya sake ni.” Ta ce bayan ta koma gidansu ne iyayenta da hadin gwiwar kungiyar Zawarawa da Marayu ta kasa suka shigar da kara gaban kotu don a bi mata hakkinta a wajen tsohon mijinta.
Ita ma amaryar ta shigar da karar Mansur Musa a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Lardi da ke Nomansland don neman ya sake a lokacin, inda alkalin kotun Mai shari’a Faruk Ahmed ya raba aurensu ba tare da ta biya shi ko sisin kwabo da sunan kudin aure ba.