… Zai nada Zainab Bulkachuwa Shugabar Kotun daukaka kara

Shugaba Goodluck Jonathan ya mika sunan Mai shari’a Zainab Bulkachuwa ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da ita a matsayin Shugabar Kotun daukaka kara ta Tarayya.Hajiya Bulkachuwa da ma alkali ce a kotun kuma ita take rikon shugabancin kotun tun cikin watan Nuwamban bara bayan ritayar Mai shari’a dalhatu Adamu.Idan majalisar ta tabbatar mata da mukamin, […]

… Zai nada Zainab Bulkachuwa Shugabar Kotun daukaka kara

Shugaba Goodluck Jonathan ya mika sunan Mai shari’a Zainab Bulkachuwa ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da ita a matsayin Shugabar Kotun daukaka kara ta Tarayya.
Hajiya Bulkachuwa da ma alkali ce a kotun kuma ita take rikon shugabancin kotun tun cikin watan Nuwamban bara bayan ritayar Mai shari’a dalhatu Adamu.
Idan majalisar ta tabbatar mata da mukamin, za ta shugabanci kotu ta biyu mafi girma a kasar na a bayan Kotun koli a daidai lokacin da mace ta farko take rike da mukamin Babban Jojin Najeriya wato Hajiya Maryam Aloma Mukhtar, wadda Shugaba Jonathan ya nada a shekarar 2012.
Hajiya Zainab Bulkachuwa, an haife ta a Gombe a shekarar 1950 kuma ta fito daga zuriyar fitaccen masanin nan marigayi Dokta Aliyu Abubakar kuma mahaifinta shi ne marigayi Malam Abubakar Gidado El-Nafaty.
Ta fara aikin lauya a shekarar 1976 kuma ta taba zama alkali a Babbar Kotun Jihar Bauchi kafin ta zama Babban Jojin Jihar Gombe, kuma ta zama alkali a Kotun daukaka kara a shekarar 1998.
daya daga cikin shari’o’in da suka fito da ita ita ce shari’ar takaddamar zaben Gwamnan Jihar Sakkwato na shekarar 2007.
Kafin Shugaban kasa ya nada ta, ita ce alkalin Kotun daukaka kara ta shiyyar Abuja, kuma ana sa ran za ta kai shekarun yin ritaya a shekara ta 2020.