Zai rika biyan matarsa Naira miliyan biyu a wata don kaurace mata
Wata kotu a Delhi ta umarci wani miloniya da ya kaurace wa matarsa ya rika biyanta kudin dawainiyar kanta da ya kai Rs400,000 (Dh23,000), wato daidai Naira milioyan biyu da dubu 300, tare da karin kashi 15 cikin 100 a kowce shekara saboda tafiyar da ya yi ya barta da karamar ’yarsu. Kotun ta yanke […]
Wata kotu a Delhi ta umarci wani miloniya da ya kaurace wa matarsa ya rika biyanta kudin dawainiyar kanta da ya kai Rs400,000 (Dh23,000), wato daidai Naira milioyan biyu da dubu 300, tare da karin kashi 15 cikin 100 a kowce shekara saboda tafiyar da ya yi ya barta da karamar ’yarsu.
Kotun ta yanke hukuncin ne bisa la’akari da cewa minjin matar yana cikin jerin hamshakan attajiran da mujallar masu kudi ta kimanta dukiyarsu, inda aka ruwaito a hada-hadar kasuwanci yana juya Rs 1,000 crore, wato kimanin kudin Indiya biliyan guda, daidai da Naira Biliyan 36.
Wani babban alkali Narottam Kaushal a kotu ya tabbatar masa da karin kashi 15 cikin 100 don daukar dawainiyar matar da ’yarta, inda ya yi nuni da cewa an samu “dimbin kari” a kudin shigar mijin a shekaru biyu na hada-hadar kasuwanci, al’amarin da bai kamata a yi watsi da shi ba.
“Jerin iyalan hamshakan attajirai da dimbin dukiyarsu wadd ta kai Rs921 crore an wallafa ne a mujallar Fortune 500, inda aka yi nuni da cewa mijin wannan m atar yana sahun iyalai masu dimbin dukiya a kasar Indiya,” a cewar alkalin, inda ya yi nuni da cewa: “shi kadai ne dan da ke zaune tare da mahaifinsa.”
“wadda takai wannan kara ba za a iya hanata hakkinta ba, bisa la’akari da karin kudin shigar da mijin ya samu,” inji alkali.
Sai dai wannan miji ya yi togaciya da cewa shi darakta ne a kamfanoni, amma albashinsa na wata bai wuce Rs 90,000 a kamfani guda.