Zai saki matansa idan suka bari aka yi wa ’ya’yansa allurar shan-inna

Allurar rigakafin cutar shan-inna da ake bayarwa lokaci-lokaci ga yara ’yan kasa da shekara biyar ta hadu da kin amincewa a wasu sassan Jihar Sakkwato da Aminiya ta ziyarta.Wani magidanci mai suna Ila Alhaji Hamza ya yi barzanar sakin matansa biyu muddin suka bari aka yi wa ’ya’yansa allurar rigakafin shan inna.daya daga cikin masu […]

Zai saki matansa idan suka bari aka yi wa ’ya’yansa allurar shan-inna
Zai saki matansa idan suka bari aka yi wa ’ya’yansa allurar shan-inna

Allurar rigakafin cutar shan-inna da ake bayarwa lokaci-lokaci ga yara ’yan kasa da shekara biyar ta hadu da kin amincewa a wasu sassan Jihar Sakkwato da Aminiya ta ziyarta.
Wani magidanci mai suna Ila Alhaji Hamza ya yi barzanar sakin matansa biyu muddin suka bari aka yi wa ’ya’yansa allurar rigakafin shan inna.
daya daga cikin masu yin allurar rigakafin mai suna Ummu Ladan ta shaida wa Aminiya cewa, sun gano haka ne lokacin da suka shiga magidancin da ke Unguwar Makera a karamar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato.
 Ummu Ladan wadda ke jagorantar ayarin masu gudanar da allurar ta ce shigarsu gidan ke da wuya don aiwatar da aikinsu take matan suka dakatar da su tare fada musu cewa mijinsu ba ya nan kuma ya sanya dokar kada a diga wa ’ya’yansu allurar kuma in sun sake aka yi ya yi alkawarin sakinsu.
Wani da ya hana a yi wa ’ya’yansa allurar mai suna Shehu Aliyu, ya shaida wa Aminiya cewa, “Ba zan bari a yi wa ’ya’yana wannan allurar ba, domin duk wani abin amfani ba a ba mu kamar takin zamani da shinkafa da sauransu sai kawai wannan, don haka ni ban bukata kwanan nan na zo asibiti da dana na saya masa maganin da duk ake so.”
A karamar Hukumar Wamakko ma an samu wadanda ba sa so a yi wa ’ya’yansu kamar yadda aka samu bayani a wurin tattara bayanan aikin da ake yi a kullum a cibiyar karamar hukumar.
A karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu, jami’an rigakafin da suka fahimci mutane ba sa son allurar, sai suka fito da hanyar shafa wa yara fenti a hannu su wuce gaba, ta yadda koda masu zagaye sun hadu da yaran za su dauka an yi musu, matakin da mutanen bangaren suke yaba shi domin a wurinsu an taimake su saboda har yanzu suna kallon allurar tana da matsala ga ’ya’yansu.
A karamar Hukumar Gwadabawa, manajan rigakafin Muhammad Nasiru Umar ya ce suna tsammanin a kwana hudu za su diga wa yara dubu 104 allurar, kuma ba su da wata matsala da ta wuce ta wutar lantarki.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi