Zai yi aure da gudunmawar fidar zuciyar dansa
Iyayen wani yaro mai suna Aliyu Tanimu da ke samun yin numfashi da kyar da taimakon abin karin numfashi na ‘odygen’ a dakin kula da marasa lafiya da ke bukatar kulawa na gaggawa na yara a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, saboda ciwon zuciya da ke damunsa, suna fada da juna a kan kudin […]

Iyayen wani yaro mai suna Aliyu Tanimu da ke samun yin numfashi da kyar da taimakon abin karin numfashi na ‘odygen’ a dakin kula da marasa lafiya da ke bukatar kulawa na gaggawa na yara a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, saboda ciwon zuciya da ke damunsa, suna fada da juna a kan kudin taimakon maganinsa.
Aliyu, wanda aka haifa kimanin shekaru hudu da suka wuce, ya fara rashin lafiya ne tun yana dan shekara daya. Bayan an yi bincike, sai aka gano akwai wani rami a cikin zuciyarsa, wanda za a iya gyarawa ta hanyar yin aiki.
Tun da aka tabbatar da cewa aikin ba zai yiwu a kasar nan ba, likitoci suka bukaci a mayar da shi wani asibiti a kasar Indiya, inda aka yi lissafi za a kashe Naira miliyan biyu kan aikin. Sai dai tun daga wancan lokaci, tsawon shekara biyu ke nan, ake jigila da Aliyu tsakanin gida da asibiti, saboda iyayensa ba su samu kudin da ake nema ba.
Saboda a samu kudin tafiya don yin maganin, asibitin AKTH ya rubuta wa iyayen yaron wasikar neman taimako, wacce a ciki aka yi bayanin yanayin ciwonsa da kuma yawan kudin da ake bukata don yi masa magani a kasar Indiya. Zuwa yanzu iyayen yaron sun dan samu wadansu kudi ta hanyar taimako, duk da cewa ba su kai yawan da ake bukata ba.
Sai dai kuma uwar yaron mai suna Malama Hussaina Yakubu tana zargin uban yaron da karkatar da kudin zuwa aljihunsa, a maimakon ceto rayuwar dan nasu, wanda shi ke nan da su. Ta shaida wa Aminiya cewa tana zargin uban yaron da yin amfani da kudin wajen gina dakin da zai sanya sabuwar amaryarsa.
A lokacin da take tattaunawa da Aminiya a Asibitin Aminu Kano, inda yaron yake kwance yana karbar magani, ta bayyana cewa ta tabbatar da cewa mahaifin yaron ya karbi kudi sama da Naira dubu 500 daga wajen mutane daban-daban. “Na tababtar a tsawon shekaru biyu da asibitin nan ya ba mu takardar nan, uban yaron nan ya karbi sama da Naira dubu 500 a hannun mutane, a cikin garin Kano da kuma mahaifarsa Sakkwato. Ban da kudin da ya samu daga mutane daban-daban a Kano, wanda yawansu ya kai Naira dubu 200, da muka je Sakkwato wani kwamishina ya ba shi Naira dubu 150, haka kuma Shugaban karamar Hukumar Bodinga ya ba da wadansu kudi masu yawan gaske, sai dai abin takaici a lokacin da muka dawo Kano da na nemi a kai ajiyar kudin banki, sai ya shaida min cewa ai ya yi amfani da kudin ya gina daki a cikin gidansu a Sakkwato inda zai sanya matar da zai aura.” Inji ta.
Ta kara da cewa, saboda ganin yanayin jikin yaron ya sanya ta kasa rufe bakinta game da halayyar mijin nata da kuma kafewar da ta yi cewa sai lallai an kai kudin banki: “Hakan ya jawo ya sake ni wai ina damunsa a kan abin da bai kai ya kawo ba. Lokacin kuma da na gaya masa cewa zan dauki yaron na kai shi wurin mutanen da suka ba shi kudin nan na shaida musu yadda ya kashe kudin, sai ya yi barazanar kashe ni, inda ya yi rantsuwa idan har na aikata hakan shi kuma sai ya biyo ni har gidan iyayena ya kashe ni.”
A cewarta, mahaifin yaron ya yanke shawarar kashe kudin ne lokacin da wani likita ya shaida masa cewa ramin da zuciyar yaron ta yi zai iya warkewa idan ya samu allurar wata guda ba sai an yi masa aiki ba.
Yayin da yake musanta zarge-zargen da Malama Maimuna ta yi masa, mahaifin yaron Malam Tanimu Aliyu ya bayyana wa Aminiya cewa duka-duka taimakon kudin da ya samu bai kai Naira dubu 200 ba. Haka kuma duk da cewa yana shirye-shiryen yin aure, nan ba da dadewa ba, amma ba da wannan kudin zai yi auren ba.
Malam Tanimu ya kara da cewa, tsohuwar matar tasa na fadin wadannan zarge-zarge ne saboda kawai ya sake ta. “Duk abin da ta gaya muku babu gaskiya a ciki. Na kalubalance ta da ku gaba daya ku je ku samu duk mutanen da ta ambata sun bayar da taimako, ku tambaye su nawa suka ba ni? Idan kuka kirga duk kudin da suka bayar za ku ga ba su wuce Naira dubu 180 ba.” Inji shi.
Mahaifin yaron ya kara da cewa, yana nan yana aiki tukuru don ya samu kudin da zai yi auren: “Gaskiya ne ina shirye-shiryen yin aure, saboda ba zan ci gaba da zama haka ba tare da mata ba. Sai dai ina tabbatar muku da cewa ba da kudin maganin wannan yaron zan yi ba. Zan yi amfani da kudin da nake nema daga sana’ata ta fawa. Ni mahauci ne da nake sayar da nama da kaji.’’
Haka kuma ya musanta zargin da ta yi masa na cewa yana yi mata barazana zai kashe ta, inda ya ce shi mutum ne mai son zaman lafiya tsawon rayuwarsa.