… Zai yi kwana 21 a dakin al’ada kafin a mika masa sandar sarauta\

Jagoran dakin tsafin Isoro a cikin fadar Ooni, Oba Olajide Ifaloba ya yi watsi ne da jita-jitar cewa za a yi tsafin jinin mutum kafin a mika sandar sarauta ga sabon sarki. Ya ce za a gudanar da dukkan abubuwa na al’ada ne a cikin dare. Kamar yadda ya ce: “Abu na farko shi ne, […]

… Zai yi kwana 21 a dakin al’ada kafin a mika masa sandar sarauta\
… Zai yi kwana 21 a dakin al’ada kafin a mika masa sandar sarauta\

Jagoran dakin tsafin Isoro a cikin fadar Ooni, Oba Olajide Ifaloba ya yi watsi ne da jita-jitar cewa za a yi tsafin jinin mutum kafin a mika sandar sarauta ga sabon sarki.

Ya ce za a gudanar da dukkan abubuwa na al’ada ne a cikin dare. Kamar yadda ya ce: “Abu na farko shi ne, shigowar sabon Ooni cikin gari da zai dumfari gidan mahaifinsa kai tsaye. Daga nan ne zai matsa zuwa dakin Ilofi da zai yi kwanaki 21 a kulle a maimakon wata uku, ana yi masa magungunan al’ada da aka yi gado kaka da kakanni a cikin dakin. Bukukuwan al’adun gargajiya na Olojo da aka saba yi a kowace shekara, sun zo daidai da wannan lokaci; shi ne dalilin da ya sa aka rage kwanakin daga wata uku zuwa kwanaki 21 da sabon Ooni na Ife zai yi a cikin wannan daki.”
Tun da farko dai, Gwamnan Jihar Osun Ogbeni Rauf Aregbesola ya tabbatar da nadin Yarima Enitan Adeyeye Ogunwusi mai shekaru 40 a matsayin sabon Ooni na Ife da zai maye gurbin Oba Okunade Sijuwade wanda ya mutu a ranar 28 ga watan Yuli.
Bayanin nada sabon Sarkin na Ile Ife yana kunshe ne a cikin takardar sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Moshood Adeoti ya sanya wa hannu da aka raba ga kafofin labarai a Litinin da ta gabata.
Kamar yadda Aminiya ta kalato, kwanaki biyu kafin fitowar sanarwar nada sabon Oonon, sai da aka girke jami’an tsaro da suke shawagi a sassa daban-daban na garin Ile Ife. Haka kuma jim kadan bayan da labarin nadin sai dimbin mutane maza da mata suka rika tururuwar zuwa gidan mahaifin sabon Ooni, Pa Ropo Ogunwusi domin taya shi murna.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani, mahaifin sabon Oonin ya ce: “A wani lokaci da muke zaune a birnin Ibadan kafin a haifi dan namu, wani mutumi mai tsoron Allah ya shaida mana cewa ba da dadewa ba za mu haifi jariri mai albarka da jarumta a rayuwarsa ta duniya. Saboda haka nake mika godiya ga Allah da Ya bayyana mana hasashen wancan mutumi a yanzu. Mun godewa Allah da Ya zabo shi daga cikin mutane 43 da suka nemi hayewa bisa wannan karaga.”
Ya roki dukkan al’ummar masarautar Ife da su yi dukkan abin da suke iyawa wajen taimakawa sabon sarki da shawarwari da za su kai shi ga sauke nauyin da aka aza masa na jagorancin kabilun yarbawa.
Shugabannin Majalisun Tarayya, Dokta Abubakar Bukola Saraki da Yakubu Dogara da Mataimakinsa Yusuf Lasun da Gwamnan Jihar Legas Mista Akinwunmi Ambode da tsohon Gwamnan Jihar Oyo Adebayo Alao Akala suna daga cikin manyan mutane da suka fara aikawa da sakon taya murna ga sabon Ooni na Ife. Shi ma Sakataren jam’iyar PDP na kasa, Farfesa Adewale Oladipo ya aika da irin wannan sako na taya murna.