Zai yi kyau a kyale dillalan man fetur su rika shigo da mai suna sayarwa a farashin da suke so?
A ba ’yan kasuwa dama – Salisu Hapijo Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja Salisu Haladu Hapijo: “Gaskiya ina goyon bayan a bai wa ’yan kasuwar fetur dama su rika shigo da mai suna sayarwa kan farashin da kasuwa ta kama, tun da matatunmu na cikin gida sun gaza su kosar da mu, ai sai mu […]
A ba ’yan kasuwa dama – Salisu Hapijo
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Salisu Haladu Hapijo: “Gaskiya ina goyon bayan a bai wa ’yan kasuwar fetur dama su rika shigo da mai suna sayarwa kan farashin da kasuwa ta kama, tun da matatunmu na cikin gida sun gaza su kosar da mu, ai sai mu dangana mu kuma dogara da ’yan kasuwa. Komai zai yi sauki idan akwai gasa tsakaninsu. To, sai dai kuma a kula sosai kada su fake da shigo da mai su rika shigo da muggan magunguna da makamai a fakaice. Muna goyon bayan yunkurin dangote a kan gina gagarumar matatar mai da za ta saukaka mana samun mai a gidajen mai. Allah Ya taimaki shugabanninmu su gudanar da mulki yadda talaka zai more, ya yi walwala, amin.”
Bai kamata ba – bilian Murray
Daga Amina Abdullahi, Yola
bilian Murray: “Bai kamata ba domin akwai masu aikin kawo man a gwamnatance. Masu aikin nan ne ya kamata su rika turo man fetur a kowace jiha na kasar. Dillali dai riba yake nema domin duk yadda ya sayar da nasa man fetur, baya taba fadi. Talaka shi ne wanda yake shan wuya. Amma dillali sai dai ya yi ta saka kudi a kan farashin da ya masa daidai. Ya kamata gwamnati ta dauki mataki a kan masu yin irin wannan halin ne. Idan har gwamnati na son aiko man fetur, dole ne ta tabbatar da cewa akwai ma’aikatar man fetur na kasa tare da su domin su sa ido a kan yadda ake gudanar da man fetur din.”
Gaskiya hakan bai dace ba – Mukhtar Abdullahi
Isiyaku Muhammed
Mukhtar Abdullahi: “Gaskiya barin ’yan kasuwa su yi yadda suke so bai dace ba. Yawancin ’yan kasuwa riba kawai suke tunani ba wai yadda za su rage wa talaka radadin talauci ba. Idan aka ce su sayo man fetur din su sayar yadda suke so, za su tsawwala wa talaka, kuma talaka zai shiga cikin matsatsi.”
Bai dace a ba ’yan kasuwa dama ba – Ibrahim London Boy
Bashir Yahuza Malumfashi, a Abuja
Ibrahim London Boy Jigirya: “Hakika bai dace a ba ’yan kasuwar fetur damar su shigo da mai ba, domin su sayar yadda suka ga dama. Dalilina kuwa shi ne, gwamnati na da ikon samar da mai wadatacce da zai maganin matsalar. Kamata ya yi duk shekara ta tsaida farashin man ga ’yan kasuwar man yadda ya dace da yanayi da zamanin yadda kasuwa ta kama. Idan kuma sun ki bin wannan tsarin, to gwamnati ta kara yawaita gidajen man NNPC a dukkan jihohi, ta hanyar karbar hayar gidajen man, domin magance matsalar.”
Bai dace a bar dillalai su yi abin da suke so ba
– Hebron Giwa
Daga Amina Abdullahi, Yola.
Hebron Giwa: “Bai dace ba, domin idan aka bar dillalan man fetur suka yi abin da suke so, ba za a sami nasarar abin da ake so a Najeriya ba. Abin da ya kamat shi ne, idan dillalan man fetur sun shigo da mai, ya kamata a yi amfani da farashin gwamnati domin komai ya tafi daidai. Amma idan aka barsu suna sayar da shi a kan farashin da suke so, za a samu damuwa a kasar. Amma idan kuma aka sayar da shi a kan farashin gwamnati, za a sami walwala sannan talaka zai ji dadi.”
Akwai matsala idan aka yi haka – Abdullahi Idris
Isiyaku Muhammed
Abdullahi Idris: “Idan aka bar ’yan kasuwa suka samu yadda suke so, kashe mutane za su yi. Kamata ya yi gwamnati ta kara yawan gidajen mai mallakarta a duk lungu da sakon Najeriya, sannan ta gyara matatun man da muke da su, sannan kuma ta tabbatar ana raba man yadda ya kamata. Idan aka yi haka sai suma ’yan kasuwa su rika shigo da man suna sayarwa. Wannan ne zai sa a samu man sosai, sannan kuma mutane su zabi inda za su saya.”