Zai yi wahala a yi sulhu da ‘Yan Neja-Delta – Bello Kirfi

daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Muhammadu Bello Kirfi Wazirin Bauchi ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya su dauki mataki mai tsauri kan tsagerun Neja-Delta da suke fasa bututun mai da gas a yankinsu. Alhaji Bello Kirfi ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a gidansa da ke […]

Zai yi wahala a yi sulhu da ‘Yan Neja-Delta – Bello Kirfi
Zai yi wahala a yi sulhu da ‘Yan Neja-Delta – Bello Kirfi

daya daga cikin dattawan Arewa Alhaji Muhammadu Bello Kirfi Wazirin Bauchi ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya su dauki mataki mai tsauri kan tsagerun Neja-Delta da suke fasa bututun mai da gas a yankinsu.
Alhaji Bello Kirfi ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a gidansa da ke Bauchi a ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce: “Muna Allah wadai da tsagerun Neja-Delta masu fasa bututun mai kuma ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin Tarayya su fahimci cewa ba a gwaninta ga irin wadannan mutane, domin duk abin da za a yi musu a banza ne saboda makafi ne ba sa gani.”
Alhaji Bello Kirfi ya kara da cewa: “Marigayi Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduw ya kirkiro musu da Ma’aikatar Raya yankin Neja-Delta da wasu ayyuka na raya yankin, kuma a lokacin mulkin Goodluck Jonathan sun lafa ba sa fasa bututun mai, amma yanzu da suka ga dan Arewa ne yake mulki sai suka sake daukar makami. Zai yi wahala a yi sulhu da mutanen Neja-Delta domin akwai wadanda suke daure musu gindi suke ba su miyagun makamai suke fasa bututun man fetur.”
Alhaji Bello Kirfi wanda ya ce su ne suka kafa Jam’iyyar PDP amma sun fice daga cikinta ne sakamakon yadda ake dauki-dora kuma ba a bin ka’ida wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Game da shekara daya na gwamnatin Shugaba Buhari Alhaji Bello Kirfi ya ce: “Na gamsu da yadda Shugaba Buhari yake tafiyar da Najeriya, sai dai kuma ya gaji dimbin matsaloli saboda tsohon Shugaban kasa Jonathan ya lalata harkokin mulkin Najeriya kuma ya ki bin ka’ida wajen tafiyar da gwamnatinsa, wanda a sakamakon haka ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari yake shan bakar wahala wajen tafiyar da mulkin kasar nan a yanzu.”
Wazirin na Bauchi ya ce an sace biliyoyin Naira a zamanin Jonathan kuma ya gagara magance matsalar tsaro da ta addabi yankin Arewa maso Gabas, sannan jihohi da dama ba sa iya biyan albashi ga ma’aikatansu.
Sai ya bayyana cewa dukkan matsalolin da suka addabi kasar nan a halin yanzu ya kamata jama’a su fahimci ba laifin Buhari ba ne, gwamnatin da ya karbi mulki daga wajenta ta haddasa matsalar ga shi yanzu kowa yana ji a jikinsa.
“Ina rokon jama’a su ci gaba da addu’a tare da ba da goyon baya ga Shugaban kasa Buhari domin ya zo da manufofi masu kyau na ingata rayuwar al’umma baki daya kowa ya san cewa Jonathan ya lalata Najeriya. Ma’aikatan Najeriya sun lalace babu abin da suka iya sai satar kudin gwamnati, kuma mafita ga talaka shi ne ya koma gona domin shi ne tushen arziki,” inji Bello Kirfi.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland