Zai yi watsi da ’ya’yansa saboda matarsa ta guje masa
Wani mutum mazaunin Unguwar Gayawa a karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano mai suna Yusuf Ibrahim yana kokarin watsi da’ya’yansa biyu, inda ya ce ba zai iya ci gaba da kula da su ba. Yusuf Ibrahim mai shekara 38 ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda guje masa da matarsa ta yi kuma ga halin […]
Wani mutum mazaunin Unguwar Gayawa a karamar Hukumar Ungogo, Jihar Kano mai suna Yusuf Ibrahim yana kokarin watsi da’ya’yansa biyu, inda ya ce ba zai iya ci gaba da kula da su ba.
Yusuf Ibrahim mai shekara 38 ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda guje masa da matarsa ta yi kuma ga halin matsin rayuwa da yake fama da shi.
Malam Yusuf wanda a yanzu haka yake zaune a shagon wani gida tare da ’ya’yan masu shekara uku zuwa biyar, ya ce tunda suka rabu da matarsa ta dawo masa da ’ya’yan shekara biyu da suka gabata yake fadi-tashi da su, saboda a danginsa ya rasa wanda zai rike masa yaran.
A cewar Malam Yusuf “Idan ban da Musulunci wallahi da tuni na watsar da yaran nan, ba wai don ba na son su ba, sai don ba zan iya ci da kula da su ba. A farkon rabuwarmu da matata ina rike da da daya mai shekara biyar sai ta sake dawo min da daya ’yar mai shekara uku. Ni nake yi musu komai kafin na fita neman abinci. Baya ga renonsu da ke kaina, a gefe guda ga shi harkoki ba su tafiya sosai, domin a yanzu haka a shagon wani gida muke kwana ni da yaran da wasu mutane, saboda ba zan iya biyan kudin hayar gida ba. Shi ya sa na fito na bayyana wa jama’ar unguwar cewa idan da wanda yake ganin yana son rikon yara, to ga nawa, don ni dai a halin da nake ciki ba zan iya rike su ba.”
Malam Muhamamd Saminu Assahabu shi ne Shugaban bangaren Da’awah na Hukumar Hisba a Jihar Kano ya bayyana wa Aminiya cewa bayan sun samu labarin matakin da mutumin ya dauka na rabuwa da yaran, sai suka nemi shi, inda ya nanata musu cewa ba shi da halin da zai iya daukar nauyin ’ya’yan.
Malam Asshabu ya ce da farko hukumarsu ta nemi ’yan uwan mutumin inda ta samu wata ’yar uwarsa ta nemi ta karbi ’ya’yan ta rike su saboda Allah, amma kememe ta ki. “Ta ce ba za ta taba rike masa ’ya’ya ba, saboda a cewarta dan uwan nata ba ya da kirki, haka zalika ba su yi zaman lafiya tsakaninta da uwar ’ya’yan ba,” inji shi.
Malam Asshabu ya ce tun a waccan rana Darakta Janar na Hukumar Hisba ya taimaka wa mutumin da kudi da kayan abinci don rage masa radadin halin da yake ciki. “Bayan Daraktan ya taimaka masa da kudi da kayan abinci, a yanzu kuma Hisba na kokarin ganin ta sami dangin matarsa ko za su iya karbar ’ya’yan su rike, idan son samu ne muna so mu yi masa bikon matar tasa don ta dawo ta rike ’ya’yanta,” inji shi.