Zai yiwu a hana bara a Najeriya?

A cikin watan jiya ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta shiga jerin jihohin da suka hana bara a kasar nan. Bisa la’akari da haka ne, mu ke tunanin ko zai yiwu a iya hana bara a Najeriya? Ga abin da jama’a suka bayyana game  da batun: Bai dace a yi haka ba – Abdullahi Bindawa Daga […]

Zai yiwu a hana bara a Najeriya?
Zai yiwu a hana bara a Najeriya?

A cikin watan jiya ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta shiga jerin jihohin da suka hana bara a kasar nan. Bisa la’akari da haka ne, mu ke tunanin ko zai yiwu a iya hana bara a Najeriya? Ga abin da jama’a suka bayyana game  da batun:

Bai dace a yi haka ba – Abdullahi Bindawa

Daga Hamza Aliyu, a Bauchi

Alhaji Bashir Yusuf Baba: “A fahimta ta za a iya hana bara a Najeriya, amma  idan za a hana bara ya kamata masu baran a samar musu da wasu hanyoyin da za su samu abin da zasu ci da kuma ba su wani tallafi na sana’oi idan an samar musu da wadannan abubuwa dana lissafa. Amma ba zai yiwu ba ka taimake ni ba, sai kuma ka toshe mini hanyar da nake samun abin da zan ciyar da iyalina ba.”

Zai yiwu don addini ya hana – Abubakar  dandada

Daga Hamza Aliyu,a Bauchi

Malam Abubakar dandada: “Zai yi wu a hana bara a kasar nan  domin addini kansa ya hana bara. Don haka bara haramun ce ga mutum mai koshin lafiya, karancin ilimi na daya daga cikin abubuwan da ya haifar da dabi’ar bara a Najeriya. Duk malamin da ya ce akwai bara a Musulunci ya fadi son zuciyarsa ne.”

Za a iya sai dai… -Bashir Baba

Daga Adam Umar, Abuja

Malam Ahmad Abdullahi: “Idan hukuma za ta tilasta wa mawadata ba da zakkah sannan a rabata ga wadanda suka cancanta, wannan ya kunshi tantance mawadata da kuma tantance wadanda suka dace su yi baran. Wasu na yin baran nan ne bisa dole a sakamakon nakasa ko kuma rashin abin yi, idan sun samu taimako sai su dauki nauyin iyalansu. Wasu kuma sun mallaki abin hannu, amma baran ta zame masu jaraba ko mai wadatarsu, ba za su daina barar ba.

Zai yiwu idan akwai aikin yi  – Malam  Hamza

Daga Adam Umar, Abuja

Malam Hamza Abdullahi: “Bara ta nakasa ko ta mutuwar zuciya akasari ana yinsu ne a sakamakon rashin aikin yi, idan hukuma ta sama wa jama’arta aikin yi, mai nakasa da ke barar yau da kullum a bainar jama’a a koyar da shi aikin yi da ya dace da nakasarsa. Haka nan shi ma mai mutuwar zuciya da ke gabatar da kuka ga jama’a ya na neman taimako ko maula, shi ma a taimaka masa da abin yi sannan ya ajiye girman kai, to bara za ta hanu.”

Hana bara zai yiwu – Abdullahi Umaru

Daga Hussaini Isah, Jos

Malam Abdullahi Umaru: “Hana bara zai yi wu saboda gwamnati tana da karfin da za ta hana yin barar. Kuma tana da karfin da za ta tallafa wa musu barar, su rike kansu ba tare da sun yi barar ba. Kuma  gwamnatocin da suka sanya dokar, ba sun yi haka ne don su takurawa masu barar ba. Sun sanya dokar ne saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar nan musamman a yankin Arewaci. Amma ya kamata gwamnatoci su dauki matakan tallafawa mabaratan kafin
su sanya dokar hana yin bara a jihohinsu. Idan aka tallafa wa musu bara suma za su tallafa wa gwamnatocin da suka hana yin baran. Don haka ina kira ga jama’a su bai wa gwamnatoci gayon baya da hadin kai.”

Zai yiwu amma… -Malam Chidawa

Daga Hussaini Isah, Jos

Malam Kabiru Muhammad Chidawa: “Tabbas hana bara abu ne da zai yi wu a kasar nan, amma sai an kula da wasu hakkoki. Kuma addinin Musulunci bai yarda da
kaskanci da roko da bara ba. Don haka hana bara zai yi wu a Najeriya. Sai dai ina kira ga gwamnatoci idan har za su hana bara, a kasar nan, to ya zaman to an kama masu barar an sanya su a makaranta a koya masu sana’o’i. Idan gwamnatoci suka yi haka hana bara zai yi wu.’’