Zai yiwu a tsame addini da kabilanci a harkar siyasar Najeriya kuwa?

Yanayin yadda jama’an Najeriya suke sanya siyasa a duk al’amuran da suka shafi kasar nan, akwai matukar damuwa. A kan sanya addini da kabilanci a bangarori masu muhimmanci irin tsaro da tattalin arziki. An dade ana maganganu a kan yiwuwar tsame addinin da kabilancin a cikin siyasar, amma kullum wasu suna ganin dole fa kowa […]

Zai yiwu a tsame addini da kabilanci a harkar siyasar Najeriya kuwa?

Yanayin yadda jama’an Najeriya suke sanya siyasa a duk al’amuran da suka shafi kasar nan, akwai matukar damuwa. A kan sanya addini da kabilanci a bangarori masu muhimmanci irin tsaro da tattalin arziki. An dade ana maganganu a kan yiwuwar tsame addinin da kabilancin a cikin siyasar, amma kullum wasu suna ganin dole fa kowa ya lura da addini, domin a tunaninsu kowane tsunstu kukan gidansu yake yi. Amma ganin yadda hakan ke janyo tabarbarewar shugabanci a kasar nan, hakan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane domin jin ra’ayinsu:

Zai iya yiwuwa- Muhammad Auwal Saleh

Daga Adam Umar, Abuja

Muhammad Auwal Saleh: “Zai iya yiwuwa idan shugabanninmu sun cire son zuciya, sannan a samu daidaito a tsakaninsu da malaman addini a kai, ta yadda za a rika fadakar da jama’a tare da nuna masu muhimmancin cancanta fiye da komi a maimakon la’akari da makusantansu kawai. A kuma nunawa al’umma cewa hakan shi ne zai kawo mana ci gaban kasa tare da hadin kai da kuma magance matsaloli irin na rigingimu da a ke samu a yanzu a sakamakon kauce tsari.”

A kan addini da kabilanci aka gina siyasar- Abdul’aziz Muhammad

Daga Abbas Ɗalibi, a Ilori 

Abdul’aziz Muhammad: “A gani na lokaci ya yi nisa idan a ka ce za a tsame addini da ƙabilanci a harkan siyasar ƙasarmu, domin a kan haka aka gina ta, don haka abu ne mai wuya a lokaci guda a sauya hakan, domin da yawan ‘yan siyasar ƙasar nan da abin da suke amfani ke nan su cin ma burinsu na siyasa, a haka za ka ga ana haddasa ƙiyayya da gaba a tsakanin al’umma, idan ana son yin wannan gyara sai malumanmmu  na addini sun tashi tsaye wajen wayar da kan al’umma bisa illar  hakan sannan suma ‘yan siyasar su sauya salon su wanda hakan ba abu ne mai sauƙi ba, sai dai kawai komai nufi ne na Allah.”

Zai yiwu amma…. – Fatima Abdullahi

Ahmed Garba Mohammed, a Kaduna

Fatima Abdullahi, a yanzu haka tana karatu ne a matakin jami’a ta ce:  “kwarai da gaske za a iya cire kabilanci da addini a siyasar kasar nan amma sai mutane sun koma ga Allah.  Ma’ana sai kowa ya koma jin tsoron Allah, an cire son rai da son zuciya. A yanzu ba abin da ya fi ci wa kasar nan tuwo a kwarya irin batun nuna kabilanci da na addini.  Ina ganin idan malamai da limaman coci za su dukufa wajen yi wa mabiyansu wa’azi  game da muhimmancin hada kai don a ciyar da kasar nan gaba wajen zabo mutane adalai ko ba addini ko kabilarku daya ba, to za a iya kawar da batun addini da na kabilanci a siyasar kasar nan.  Don haka a nawa ra’ayin za a iya kawar da wannan batu amma sai an tashi tsaye.”

A gaskiya da kamar wuya – Hauwa Muhammad danjuma

Daga Adam Umar, Abuja     

Hauwa Muhammad danjuma: “A gaskiya da kamar wuya idan a ka yi la’akari da yadda siyasarmu take ta samun ci gaban mai hakar rijiya a bangaren hadin kai da kishin kasa. Saboda su kansu wadanda ya kamata su kawo gyaran su ne a gaba wajen ingiza jawo bambance-bambancen domin kawai su ci gajiyar hakan wato abin nan da bature ke cewa dibide and rule, wato kau da hankalin jama’a ta han’yan raba kansu sannan kai kuma sai ka yi ta mulkarsu ba su da lokacin nazari a kan kurakuranka.”

Ba zai yiwu ba -Malam Ibrahim Dambuwa

Daga Abbas Ɗalibi, a Legas 

Malam Ibrahim Dambuwa: “Tsame addini da ƙabilanci a siyasar ƙasar nan ba zai yiwu ba domin kuwa tsarin da ake a kai yanzu ke nan, za ka ga idan shugaban ƙasa musulmi ne, mataimakinsa kirista ne, haka idan ɗan Kudu ne shugaban ƙasa mataimakinsa ɗan Arewa a haka tsarin yake don haka mafita kawai shi ne yin haƙuri tare da mutumta juna domin ko a gidan aure ne tsakanin miji da mata idan kaga aure ya yi ƙarko to ɗaya ne ya yi haƙuri da ɗayan hakan abin yake wannan lamari sai dai addu’a

Da wuya ne in zai yiwu – Umma Sa’idu Ibrahim

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Umma Sa’idu Ibrahim:  “A nata ra’ayin game da batun cire kabilanci da na addini a siyasar kasar nan ta bayyana cewa:  “A gaskiya wannan batu da kyar in zai yiwu a ce za a iya cire batun kabilanci da na addini a harkokin siyasar kasar nan.  Hasalima idan aka lura da kyau, ai wadannan abubuwa biyu, kabilanci da addini su suka jefa kasar nan a halin da take ciki a yanzu.

A duk lokacin da aka taso da wani batu, abin da jama’a ke fara dubawa shi ne wane yare ne kai (kabilanci) ko wane addini kake bi (addini).  Don haka ko takarar siyasa wani ya fito abin da ake farawa dubawa shi ne wane yare ne shi, ko wane addini yake b? 

 In haka ne ta yaya za a iya cire wadannan abubuwa a harkokin siyasar kasar nan?  Don haka a nawa ra’ayin abin da kamar wuya…