Zai zama bakar fata dan sama jannatin farko a 2015
Wani dan Afirka ta Kudu, mai suna Mandla Maseko, ya zama bakar fata na farko da zai fara zama dan sama jannati. Wannan matashi dan shekara 25, mai shirya kayan kida ne da gyaran sauti, wato DJ a wurin bukuku, da ya samu damar zuwa sararin samaniya a shekara mai zuwa.Daga kauyen Mabopane, mai yawan […]

Wani dan Afirka ta Kudu, mai suna Mandla Maseko, ya zama bakar fata na farko da zai fara zama dan sama jannati. Wannan matashi dan shekara 25, mai shirya kayan kida ne da gyaran sauti, wato DJ a wurin bukuku, da ya samu damar zuwa sararin samaniya a shekara mai zuwa.
Daga kauyen Mabopane, mai yawan kura da ke kusa da birnin Pretoria, zai yi tafiyar kilomita 103 a sararin samaniya (mil 64) nan da badi, bayan da ya lashe gasar da cibiyar binciken sararin samaniya ta Amurka ta shirya.
Bakar fatar ya kayar da mutum miliyan, wadanda suka shiga gasar daga kasashe 75, inda aka zabo a cikin jerin mutum 23 da za a harba zuwa sararin samaniya a cikin kumbo mai lakabin Lynd Mark II.
Moseko tsohon dalibin Injiniya a fannin gine-gine, wanda dole ta tursasa shi ya ajiye karatunsa, saboda ya kasa biyan kudin makaranta. A halin yanzu zai yi tafiya a saman doron kasa, kuma zai samu kyautar Dala dubu 100 da zarar ya dawo.
Matukar dai ba a samu hamsahakan masu arziki daga bakaken fatar Afirka sun biya kudi don a kai su sararin samaniya ba, kafin nan da shekara mai zuwa, Maseko zai kasance bakar fata na farko da zai fara shiga sararin samaniya.
Wannan matashi da ke zaune a kauyensu, tare da iyayensa da kannensa hudu, an bayyana shi a matsayin wand aya lashe gasar ne a ranar 5 ga Disamba, wato sa’o’i kadan da mutuwar gwarzon alummar Afirka ta Kudu. Ya ce ya sha tunanin bakaken fari, a jerin mutanen da suka yi fice a duniya, wadanda suka hada da Mandela da Barack Obama, a matsayin shugaban Amurka bakar fata na farko. Acikin irin nishadinsa, ya yi hasashe da mafarkin tattauna da marigayi Nelson Mandela.
Cibiyar Nazarin sararin Samaniya ta Apollo, wato AdE Apollo Space Academy, ta shirya wannan gasa, da ta bai wa Maseko nasarar tafiya sararin samaniya. “a lokacin da nike dauke da cikin Mandla, na fahimci cewa zan haifi tauraro,” a cewar mahaifiyar Maseko.
Mahaifiyar Maseko mai share-share da goge-gogen makaranta ce, shi kuwa mahaifinsa kayan gyaran mota yake sarrafawa. Da ma can babbn burin Maseko ya karancin fannin Injiniyan sarrafa na’urorin jirgin sama, wato “aeronautical engineering.”
Shi kuwa Ministan Kimiyya da kere-kere na kasar Afirka ta Kudu, Derek Hanekom, yana ganin Maseko a matsayin abin koyi ga masu tasowa da ke da zimmar kwarewa a harkar sararin samaniya.
Babu wamni a cikin zuri’ar Mandla Maseko da ya taba fita daga kasar Afirka ta Kudu, amma yau ga dansu, matashi mai shirya sautin kade-kade da raye-raye zai tafi sararin samaniya, tare da kyautar kudin Amurka Dala dubu 100.