Zainab Atiku Bagudu: Mata sun fi maza rike aure

Zainab Atiku Bagudu likitar yara ce, ita ce mai asibitin gwaje-gwaje na Medicaid da ke Abuja, t ace mata ke rike aure. Ta nemi a yi karatu don a fita daga jahilcin da ya dabaibaye arewa. Tarihin rayuwataSunana Zainab Atiku Bagudu. Ni mutumiyar Zamfara ce. Maigidana mutumin Jihar Kebbi ne. An haife ni a Legas, […]

Zainab Atiku Bagudu: Mata sun fi maza rike aure

????????????????????????????????????

Zainab Atiku Bagudu Zainab Atiku Bagudu likitar yara ce, ita ce mai asibitin gwaje-gwaje na Medicaid da ke Abuja, t ace mata ke rike aure. Ta nemi a yi karatu don a fita daga jahilcin da ya dabaibaye arewa.

Tarihin rayuwata
Sunana Zainab Atiku Bagudu. Ni mutumiyar Zamfara ce. Maigidana mutumin Jihar Kebbi ne. An haife ni a Legas, na yi karatun firamare da sakandare a Legas, na yi sakandaren kueen’s College ne. Ina da kawaye daga wurare da dama wadanda suka hada da ’yan kudu da arewa. Da na gama sai na dawo Sakkwato. Duk da yake ba ni da niyyar karatu amma kawuna ya ce dole sai na yi karatun likitanci. Na yi karatun likitanci a Zariya, inda na yi shekara 5. Na yi zaman koyon aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Bayan na kammala sai na koma Birtaniya, inda na kware a lafiyar yara.  Ni likitar yara ce, amma na shiga bangaren bincike da gwaje-gwaje. Abin da nake nufi shi ne, aikin da muke yi ya fi shafar bangaren cutar da ke damun mutum. Muna da na’urori da muke sanya mutum a ciki domin binciken lafiyarsa. Har yanzu ina matsayin likitar yara ne amma aikina ya fi shafar bincike kan neman abin da ke damin mutum a cikin jikinsa.
Shakuwa tsakanin iyaye
Na shaku da iyayena gaba dayansu. Ba zan iya cewa na fi shakuwa da daya daga cikinsu ba. Akwai abubuwan da ya shafi uwa wanda za ka iya zuwa neman shawara, haka ma akwai na uba. Ni dai Alhamdulillahi. Duk suna da ransu. Saboda haka ba zan ce na fi shakuwa da daya daga cikinsu ba.
Abubuwan da na karu da su a wajen iyayena
Abin da na fi karuwa da shi a wajen mahaifiyata shi ne karatuna. Ita take matsawa ta ga na dage a kan karatu. Ta fi tsayawa a wannan bangaren. Haka ma a fannin addini. Shi kuma mahaifina, komai kake so dai zai yi. Mahaifina na biye mana kuma bai cika fada ba sai dai mahaifiyata. Kuma yana taimaka mana sosai, duk da girmanmu, idan muna son wani abu wajensa muke zuwa.
kalubale ta hanyar aiki  
Babban kalubalen da ake fuskanta musamman ma ga mata a hanyar aiki shi ne: ba zan manta ba, da nake aiki a asibiti, idan an ga mace sai a ce da ita nas, kuma namiji shi ne likita. Akwai yadda mutane ke kallonmu sai su ga bai kamata a ce mace ita ce likita ba. Kuma idan an samu marar lafiya ko namiji, idan kana son ka duba jikinsa sai ya ki. Kodayake, akwai al’ada, akwai kuma addini, wadannan dole ne su kawo matsala. Ko mun ki ko mun so akwai abin da idan mace ta yi shi kamar namiji, dole zai jawo mata illa. Kuma yadda namiji zai fito ya nemi wasu abubuwa, ba haka mace za ta fito ba. Kamar mu yanzu, muna neman wasu wadanda za su kawo mana mutane domin mu magance musu matsalolinsu, amma ba za mu iya ba saboda ni mace ce. Idan na shiga yawo a ce yau ina nan gobe ina can, sai a ce da ni ina yawo. Amma da namiji ne, ba za a gan shi a hakan ba sai ma a ce yana da kwazo.
Yadda nake hada aiki da kuma aikin gida
Akwai yadda za ka iya yi. Kuma ana aike, Allah Ya sa ina da miji wanda ya san ya kamata. Kuma wasu ayyukan gidan za ka iya neman wanda zai taimaka maka. Kuma sai Allah Ya buda maka wata hanyar sai ka yi. Gaskiya hada aiki da lura da iyali akwai wahala. Saboda kula da gida, aiki ne wanda ya kamata kana yi tun daga safe har yamma. Kuma za ka yi wanda za ka iya yi, in ka koma gida ka yi fada a kan me ya sa ba a yi sauran ayyukan ba, wanda aka yi kuma ka gode an yi.
Farin cikin zama uwa
Akwai farin ciki kwarai da gaske kuma akwai damuwa. Abu ne wanda zai kawo maka tunani a kan ka kawo mutum wanda Allah Ya ba ka ta hanyarka. Dole ka zauna ka yi nazari ta hanyar rayuwarka. Akwai farin ciki bayan haka, duk abin da ya shafi wannan rai din, kai ma ya shafe ka. Gaskiya wani abu ne wanda ya kamata kowa ya samu ya dandana wa wanda Allah Ya ba dama wanda kuma Allah bai ba dama ba, suna iya samun yara marayu, sai su dauko domin su ji yadda abin yake.
Inda nafi sha’awar zuwa hutu
Da nakan ce ina sha’awar zuwa wurare da dama, amma babu inda na fi sha’awar zuwa sai makka. Ko don na dawo daga ummura ne? Amma ina jin ina son komawa. In da hali sai in koma can da zama. Abin da ya sa nake son zuwa Makka shi ne, nakan ji wani irin kwanciyar hankali da natsuwa musamman in na ga Ka’aba. Ba zan ce na fi kowa addini ba ko kuma ni wata ustaziya ce ba. Kawai nakan ji natsuwa da kwanciyar hankali idan ina kasar Makka.
Halayen mata da ke burge ni
A gaskiya ina son in ga mace mai ilimi wadda ta san abin da take yi, kuma tana amfani da shi. Da mace wadda ta san ya kamata kuma ta san ciwon uwa, watau ciwon haihuwa. In kuka ga haka, za ku ga macen ta zama mai tausayi.
Abin da nake so a tunani da shi
Ina son a tunani a matsayin macen da ta zo ta yi iya kokarinta a bangaren lafiyar yara.

Burina
Ina son na ga kasarmu musamman ma Arewa mun samu ci gaba a bangaren neman ilimi. Saboda idan ba mu tsaya muka natsu muka nemi ilimi ba, muka kawar da jahilci ba, abubuwanmu da yawa ba za su taba tafiya daidai ba. Musamman ma mata, idan ba su tsaya suka nemi ilimi ba don su yaki jahilci ba, abubuwanmu ba za su tafi daidai ba. Ba na cikin masu cewa wai gwamnati ya kamata su yi kaza, ko za su yi kaza. Gwamnati ta gina makarantu; sai ka ga ko malaman ba za su je da wuri ba ko masu aiki ba sa zuwa aiki yadda ya kamata. Idan kuma kowa ya yi aikinsa daidai tsakaninsa da Allah, tabbas abubuwanmu za su tafi daidai. Ina fatan cewa  za mu samu zaman lafiya domin akwai damuwa kwarai da gaske a Najeriya. Muna fatan Allah Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali dangane da duk fitintunun da muke fuskanta.
Sirrin zaman aure
A gaskiya, mace ita take rike aure. Abin da zance shi ne mata su fahimci halin mijinsu, idan ka gane halin mijinka, to ka gama komai. Ka san yadda za ka zauna da shi lafiya, za ku ji ana cewa ma’aurata da su yi hakuri, wani hakurin nan ba ya yi mishi. Ya dangata da hali ne. Ya kamata mace ta karanci halin mijinta. Idan ta haddace halinsa, za a zauna lafiya. Kuma mace ta tsaftace rayuwarta da gidanta da kuma ’ya’yanta kuma kada a yi nesa da addu’a, sai a ga da yardar Allah komai sai ya tafi daidai.
Macen da nake sha’awar haduwa da ita
A gaskiya ba ta da rai amma zan so na hadu da ita. A gaskiya macen da take burge ni a cikin tarihi dai, ita ce matar Annabi (S.A.W) Khadija. Domin ita ce macen farko da ta yadda da shi kuma ta karbi Musulunci.
Shawara ga matasa da masu karatu
A gaskiya kasarmu na fuskantar raddi da dama a kowani bangare. Muna bukatar fahimtar juna, bukatar hakuri a zauna lafiya. A gane cewa duk rigingimun nan ba za su kawo mana ci gaba da zaman lafiya ba. Idan muka zauna muka gane juna, kuma muka yi abubuwan da suka kamata, kuma muka nisanci abubuwan assha da shaye-shaye da duk ayyukan banza za mu samu zaman lafiya. Kuma kasarmu za ta bunkasa.

 

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya