Zainab Mu’azu: Marainiya ’yar shekara 14 da ta kware wajen hada takalman zamani
Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanki? Sunana Zainab Mu’azu, shekarata 14, ina zaune a Unguwar bulbula da ke garin Jos a Jihar Filato. Ina aikin hada takalma ne. A bangaren karatu ban yi karatun boko ba, amma a yanzu na kammala makarantar Iftida’iyyah Islamiyya School a nan Jos, rashin gata ne ya hana […]
Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanki?
Sunana Zainab Mu’azu, shekarata 14, ina zaune a Unguwar bulbula da ke garin Jos a Jihar Filato. Ina aikin hada takalma ne. A bangaren karatu ban yi karatun boko ba, amma a yanzu na kammala makarantar Iftida’iyyah Islamiyya School a nan Jos, rashin gata ne ya hana ni yin karatun boko ba wai ba na so ba.
Aminiya: Me ya ja hankalinki har kika fara sana’ar hada takalma?
Zan iya cewa gado na yi, kasancewar mahaifina kafin ya rasu mai gyaran takalma ne, to wani lokaci idan an dora mini tallar rogo, idan na je wucewa ta wurin da yake gyara sai ya kira ni, domin ba ya so in rika fita talla, abin ya zama masa dole ne shi ya sa yake bari na in fita talla. To, duk lokacin da na je wurinsa sai ya ce in ajiye kayan tallata, sai ya ce in zauna a kusa da shi don in rika ganin yadda yake hada takalma.
Da haka, da haka har na koyi gyaran takalmi, wata rana idan na je wurinsa idan an kawo masa gyaran takalma sai ya ba ni, ya ce in gyara, idan na gyara aka ba ni kudin sai in ba shi, wani lokaci ya karba, wani lokaci ya ce in rike, a nan na fahimci muhimmanci sana’a, haka dai aka ci gaba da tafiya har Allah Ya yi masa rasuwa, inda bayan nan duk lokacin da takalmina ko mahaifiyata da kannena ko yayuna suka tsinke sai in yi amfani da kayan gyaran takalman mahaifina in gyara musu.
Da haka mutanen unguwarmu suka samu labari, inda daga nan suka fara kawo mini gyaran takalmansu. Ana haka wata rana kusan Sallah sai ba ni da takalmi, to akwai wani tsohon takalmina sai na yi masa kwaskwarima, ya yi kyau sosai, har ya dawo kamar sabo, kowa ya gani sai ya ce ya yi masa kyau, inda nan ma mutane suka rika cewa in yi musu, na rika yi musu ina karbar kudin aikina, kafin ka ce me dai na yanke shawarar fara hada sabbin takalma, shi ne ma har zuwa yanzu ina ci gaba da sana’ar hada takalma.
Aminiya: Lokacin da za ki fara hada sabbin takalma, ko kin je wurin wani ya koya miki?
A’a. Na dai fara daga daye tsohon takalmi in mayar da shi sabo ne, da haka har na kware. Wato zan je kasuwa in sayin sol din takalmi sai in yi kokarin hadawa, idan na gama sai in ga ya yi kyau.
Aminiya: Kamar wadanne kayayyakin aikin kike amfani da su?
Zainab:Ina amfani da gam da kibiya da buroshi da katafila da nora da fatoci iri-iri da guduma da man polish da injin goge takalmi da ake kira piling machine da wuka da almakashi da risho da kososhi da sauransu.
Aminiya: Kamar wadanne irin takalma kike yi yanzu haka?
Ina yin takalman mata da na maza. Na mata sun hada da foreign shoe da flat shoes. Sannan ina yin takalman yara su ma na maza da na mata.
Aminiya: A rana kikan yi kamar takalma nawa?
Nakan yi takalma kamar 10, idan har ban hadu da wani cikas ba.
Aminiya: Kamar nawa ne farashin takalman da kike yi?
Kamar Flat shoes ina sayar da su Naira 800 zuwa dubu daya, mai foreign sole kuma daga dubu daya da 500 zuwa dubu biyu, wani lokaci har dubu biyu da 500. Na maza kuma nakan sayar da su Naira dubu daya zuwa dubu daya da 500. Na kananan yara kuma sun kama daga Naira 300 zuwa 400, wani har 500.
Aminiya: Wadanne matsaloli kika fuskanta lokacin da kika fara sana’ar takalma?
Tun daga lokacin har zuwa yanzu ina fama da matsalar karancin jari, wani lokaci kuma za ka samu babu wutar lantarki da yake wani bangare na aikina ya shafi aiki da janareto ne, wato idan zan goge takalmi da injin piling machine. Wani lokaci zan yi aiki da yawa amma rashin wuta sai ya hana ni karasawa. Domin a yanzu ba ni da janareto na dogara da wutar lantarki ne, kuma kai ma ka san ba kullum ake samun wutar lantarki ba.
Aminiya: Tun yaushe kika fara sana’ar hada takalma?
Na ka kusa shekara 6 ina yi.
Aminiya: Zuwa yanzu wadanne nasarori kika cimma a harkar sana’ar hada takalma?
Ina daukar nauyin kaina, sannan ina taimaka wa ’yan uwana. Abin da zan ci, in sha, in yi sutura bai gagare ni ba.
Aminiya: Wane buri kike so ki cimma dangane da sana’ar hada takalma?
Burina in samu jari mai karfi da zan ci gaba da sana’ata har ta kai ga ta yi bunkasar da zan iya samar da kamfanin takalma da zai shahara a duniya. Sannan ina da burin a ce takalman da zan yi su zama irin takalman da za a rika yayinsu ba ma a Najeriya ba har ma da sauran kasashen duniya ciki har da Turai.
Aminiya: Yaya kike sayar da takalman da kika yi?
Ana zuwa gida a saya, sannan an taba zuwa daga Nijar da Jihar Kebbi da Abuja da kuma Kano an sayi takalman da na yi, amma yanzu saboda babu isasshen jari da kuma fama da nake da matsalar wuta, ba na iya yin takalma masu yawan da har za a saya daga sauran jihohin kasar nan.
Aminiya: Zuwa yanzu akwai wadanda suke aiki a karkashinki ko kuma wadanda kike koya wa aiki?
Babu a yanzu, kodayake da yawa mutane sun zo in koya musu aiki, amma wurin da nake ya yi kadan, hakan ya sa na ba su hakuri. Duk da cewa aikin yana yi mini yawa, amma babu halin da zan dauki wadansu, saboda wurin ya yi kadan. Idan har da gwamnati za ta taimaka mini har in kai ga bude shago to burina in taimaka wa mata su koyi sana’ar hada takalma don su taimaki kansu.
Aminiya: Wane kira kike da shi ga gwamnati?
Ina kira ga gwamnati da ta taimaka wa masu kananan sana’o’i irina don mu ci gaba da dogara da kanmu. Sannan ina bukatar jarin da zai sa in tsaya da kafafuna, kama daga kama haya ko sayen wurin da zan rika aiki kasancewar yanzu a dakin da nake kwana nake aikin hada takalman. Sannan ina bukatar kayan aiki kamar janareto da sabon injin piling machine da keken dinki da sauran kayayyakin da zan rika amfani da su, idan har gwamnati za ta taimaka mini to zan ji dadi sosai.