Zainab Nasir Ahmad: Yadda shan shayi zai kawar da shayi

An yi amanna Zainab Nasir ce mace ta farko da ta jagoranci zanga-zanga a Kano.

Zainab Nasir Ahmad: Yadda shan shayi zai kawar da shayi

Mai yiwuwa ambaton Zainab Nasir Ahmad da shayi a lokaci guda ya sa a yi tunanin tana sayar da shayi ne ko ganyen shayi ko wani abu mai kama da haka.

To ba daya. Abin da ya hada ta da shayi shi ne wani kamfe da ta kirkiro mai suna “Shayin Zaman Lafiya” (Tea for Peace a Turance) wanda a karkashinsa takan hado kan matasa su tattauna hanyoyin kawo zaman lafiya a kasa yayin da suke kurbar shayi.

Amma fa ba da wannan yekuwa Zainab ta yi fice ba. An fara sanin ta ne bayan da ta kaddamar da wata yekuwar ta samar da audugar al’ada kyauta ga ’yan matan da ke tsakanin al’ummarta.

Mutum ba zai fahimci muhimmancin wannan kokari ba sai ya san irin rudanin da ’yan mata sabbin balaga ke shiga idan suka fara jinin al’ada, musamman ma a ce ba su da abin da za su yi amfani da shi don tsaftace kansu.

Jawo hankalin da wannan yekuwa ta yi ta sa masu ruwa da tsaki da dama suka sha alwashin taimakawa – ’yan matan da Zainab ta yi abin don su kuma suka samu kwanciyar hankali.

Binciken kwakwaf

A watan Disamba na bara jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) suka turke ta a ofishinsu inda suka yi mata tambayoyin kwakwa bayan ta jagoranci wata zanga-zanga don nuna adawa da rashin tsaron da ake fama da shi a jihohin Sakkwato da Zamfara.

Wannan ya sa ta janye zanga-zangar; ya kuma sa ana yi mata kallon mace ta farko a tarihi da ta jagoranci zanga-zanga a Kano.

A yanzu haka Zainab Nasir Ahmad darakta ce a wata kungiyar matasa mai zaman kanta da ke yaki da cututtuka masu yaduwa wadda ake kira YOSPIS.

Sannan kuma ta taba zama jakadiyar zaman lafiya ta kungiyar Equal Access lokacin da gidan talabijin na National Geographic ya ba ta horo a kan dabarun daukar hoto da bayar da labari.

A watan Janairun 2022, kungiyoyin Startup Kano da Women Founders Group suka ba ta lambar yabo ta ’Yar Arewa da ta Fi Zama Abar Koyi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos