Zainab uku
Wani magidanci ne yana da mata biyu sai tafiya ta kama shi. Ya ce wa matan su shirya su tafi tare. Bayan sun shirya sun hau mota sai suka yi rashin sa’a a tafiyar tasu, ’yan fashi suka tare su; suka duk ce su fito. Uwargida na fitowa daga motar ta ce: “ooh, ni Zainab […]
Wani magidanci ne yana da mata biyu sai tafiya ta kama shi. Ya ce wa matan su shirya su tafi tare. Bayan sun shirya sun hau mota sai suka yi rashin sa’a a tafiyar tasu, ’yan fashi suka tare su; suka duk ce su fito. Uwargida na fitowa daga motar ta ce: “ooh, ni Zainab na shiga uku!” Sai ogan ’yan fashin ya ce: “Me kika ce?” Sai ta kara maimaita abin da t ace da farko. Sai ya ce: “Ku bar wannan mai sunan mahaifiyata ce.” Amaryar tana jin haka sai ta ce: “Ni ma sunana Zainab.” Suka kyale ta, suka juya suka tambayi mijin: “To kai kuma yaya sunanka?” Sai ya amsa musu da cewa: “Ni ma sunana Zainab, domin koda za mu fito yanzu daga gida sai da maigari ya ce mana: “Sai kun dawo Zainab uku!”
Daga Shehu Mustapha Chaji