Zaizayar kasa na neman raba jama’a da matsugunansu a Gombe

Al’ummar Unguwar Arawa da ke karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun koka kan yadda zaizayar kasa a rafin garin ke neman raba su da muhallinsu, inda suka bukaci gwamnatin jihar ta kai musu agajin gaggawa.Wani mai magana da yawun jama’ar unguwar Alhaji Salisu dan Iyan Arawa, ya shaida wa wakilinmu cewa rafin na neman […]

Zaizayar kasa na neman raba jama’a da matsugunansu a Gombe
Zaizayar kasa na neman raba jama’a da matsugunansu a Gombe

Al’ummar Unguwar Arawa da ke karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun koka kan yadda zaizayar kasa a rafin garin ke neman raba su da muhallinsu, inda suka bukaci gwamnatin jihar ta kai musu agajin gaggawa.
Wani mai magana da yawun jama’ar unguwar Alhaji Salisu dan Iyan Arawa, ya shaida wa wakilinmu cewa rafin na neman raba su da gidajensu tun fiye da shekara uku inda suka yi iya kokarinsu amma karfinsu yana neman karewa ba tare da nasara ba.
Alhaji Salisu dan Iya, ya ce sun yi kokarin sun kashe fadadar da rafin yake yi ta hanyar cike shi da shara da tayoyi da sauransu amma ya fi karfinsu saboda duk shekara karuwa yake yi.
Ya ce cikon da suke yi ne ya taimaka wa wasu gidajensu a unguwar, da tuni rafin ya cinye su ta hanyar kwararowar ruwa daga bayan Kwalejin Ilimi ta Tarayya zuwa garin nasu.
Ya ce hanyar shiga garin nasu guda daya ce da ta hade unguwannin Kagarawal da Malam Inna da Kundulum, kuma tana neman katse tsakanin unguwannin.
dan Iyan ya ce sun rubuta takardar koke ga gwamnatin Jihar Gombe don a kawo musu dauki amma har yanzu babu labari, inda ya ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi a kwanakin nan ya sa hankalinsu ya kara tashi domin ruwan rafin ya sake canja wata hanya inda ya raba unguwar gida biyu.
Sai ya roki gwamnatin Gombe ta gaggauta kai musu dauki don daure rafin kuma ya roki masu hannu da shuni su kai nasu daukin don ceto gidaje da rayuwar mazauna unguwar.