Zakanya ta kashe mai ba ta abinci a Iran
Zakanyar ta tsere ita da mijinta.
Wata Zakanya ta kashe mai kula da ita a wani gidan ajiyar namun dawa a kasar Iran yayin da yake ciyar da ita da wani Zakin abincin rana.
Zakanyar ta kubuce daga keji lokacin da ya ke sa musu nama ta taga, sannan ta gudu da wani Zakin da ke zaman mijinta.
- Tsantsanta bauta ta sa wani mutum ya yanke ’ya’yan marainansa a Binuwe
- Zazzabin Lassa ya kashe mutum 32 a Najeriya
Kamfanin dillancin labaran IRNA da ke kasar Iran, ya bayyana cewa marigayin mai suna Esfandani yana da shekaru 40, sai dai tuni aka kama dabbobin biyu bayan mai aukuwar ta auku.
’Yan sanda da masu gadi sun kama zakunan biyu bayan ’yan sa’o’i suna neman hanyar fita daga gidan dabbobin wanda yake a tsakiyar birnin Arak, kimanin kilomita 200 Kudu maso yammacin Tehran babban birnin kasar Iran.
Hukumomi na gudanar da bincike kan kashe mutumin da Zakanyar ta yi, ko da yake ana yawaita samun kubucewar namun jeji daga gidajen adana dabbobi a kasar Iran, kuma galibi ana zargin rashin matakan tsaro a wasu gidajen adana namun jejin na haifar da barazana.
Bayanai sun ce gidan kula da namun dajin na Arak na cikin mafi girma a kasar Iran.