Zakaran da aka fille wa kai ya rayu watanni 18

Shekara 70 da suka wuce, wani manomi a Colarado ta kasar Amurka ya sare kan zakara, wanda ya ki mutuwa har tsawon watanni 18, al’amarin da ya sanya zakaran ya shahara. Saidai abin da ya daure mutane kais hi ne ya ya aka yi ya rayu ba tare da kai ba, a cewar, Chris Stokel […]

Zakaran da aka fille wa kai ya rayu watanni 18
Zakaran da aka fille wa kai ya rayu watanni 18

Shekara 70 da suka wuce, wani manomi a Colarado ta kasar Amurka ya sare kan zakara, wanda ya ki mutuwa har tsawon watanni 18, al’amarin da ya sanya zakaran ya shahara. Saidai abin da ya daure mutane kais hi ne ya ya aka yi ya rayu ba tare da kai ba, a cewar, Chris Stokel Walker.
A ranar 10 ga Satumbar 1945l Lloyd Olsen da matarsa, suna yanka kaji a gonarsu da ke Fruita, a Colarado, sai Olsen ya sare kan daya daga cikion wadannan tsuntsaye, ita kuwa matarsa sai goge su take yi, amma daga cikin kaji 40 zuwa 50 da aka yanka, sai daya ya ki mutuwa
“Sun samu daya wanda bai mutu ba, ya ma tashi yana tafiya,” a cewar jikan wadannan ma’aurata, mai suna Troy water, wanda shi ma manomi ne a Fruita. Wannan zakara dai ya yi fuffuka ya tashi, ya kuma ci gaba da gudu.
A wannan dare sai aka sanya shi a cikin wani akwati da ake adana tuffa, ya kwana, amma da Lloyd Olsen ya tashi da safe, sai ya buda ajiyarsa don ganin abin da ya faru. “Wannan halitta dai tana nan a raye,” Inji Waters “Wannan al’amari yana cikin rikitaccen tarihin wadannan iyalai,” a cewar Christa Waters, matar Troy.
Waters ya samu wannan labarin ne a lokacin da yake karami, sa’adda kakansa ya zo ya yi jinya a gidan iyayensa. A lokacin dakinsu yana kusa da na juna, kuma kakansa ba ya iya barci, har ta kai ga yakan yi surutai na sa’o’i da dama.
Samun labarin wannan al’amari da ya auku a garin Fruita game da zakara mara kai. Sai kuma wata jarida ta tura wakili ya tattauna da shi. Kai har ta kai ga wani mai shirin wasanni, ya yi tafiyar mil 300 daga birnin Salt Lake da ke Utah, don yin shirin a kan wannan zakara. Mutunmin da ake kira Hope Wade, ya yi shirin ne da zakaran da zimmar samun kudi.