Zakarun Musabakar Izala ta kasa sun samu motoci da kujerun Hajji
Zakarun Musabakar Karatun Alkur’ani ta kasa ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa karo na 18 da aka gudanar a garin Jalingo, Jihar Taraba sun sami kyatuttukan motoci da kujerun Hajji da sauran kyaututtuka a ranar Asabar da ta gabata.Gwarzon Shekara na bana, Muhammad Bukar Zarami daga Jihar Barno ya samu mota da […]
Zakarun Musabakar Karatun Alkur’ani ta kasa ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa karo na 18 da aka gudanar a garin Jalingo, Jihar Taraba sun sami kyatuttukan motoci da kujerun Hajji da sauran kyaututtuka a ranar Asabar da ta gabata.
Gwarzon Shekara na bana, Muhammad Bukar Zarami daga Jihar Barno ya samu mota da kujerar Hajji, wanda ya zo Yusuf Sulaiman Abubakar daga Jihar Yobe shi ma ya samu
kyautar mota kirar Opel, yayin da Salim dalha Jos daga Jihar Filato da ya zo na farko a karatun Izu 60 ba tafsiri ya samu mota kirar Honda.
Sauran su ne Iliyasu Aliyu Haruna daga Jihar Barno ya zo na farko a Izu 40 ya samu mota kirar Ford, sai Abdulkarim Ibrahim Paki daga Jihar Kaduna ya zo na farko Izu 20 ya samu mota kirar Honda Cibic da tallafin karatu, shi kuma Yusha’a Sani Argungu daga Jihar Kebbi da ya zo na farko a Izu 10, ya samiu kujerar Hajji.
A jawabinsa a wajen rufe gasar Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yaba wa kungiyar kan kokarin da take yi wajen yada addinin Musulunci a kasar nan, da kuma wannan gasar da take shiryawa.
Ya ce irin wannan gasa da kungiyar take shiryawa daga matakin rassa zuwa matakin kasa zai taimaka wajen tarbiyyatar da ’ya’yan Musulmi.
Sarkin Musulmin wanda Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu
Abubakar ya wakilta, ya nanata goyan bayansa ga kungiyar, kan ayyukan da take gudanarwa.
A jawabin shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce karatun Alkur’ani yana wanke zuciya.
Sheikh Jingir ya yi kira ga ’yan siyasar kasar nan kan su hada kai, su mance da bambance- bambancen siyasar da ke tsakaninsu, su taru su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce “Ba mu da wata kasa a duniya sai Najeriya, don haka ya zama wajibi mu taru Musulmi da Kirista mu roki Allah Ya tona asirin wadanda suke kawo mana rikice-rikice a kasar nan, domin mu samu zaman lafiya.
Kuma ya yi kira ga malaman kasar kan su ji tsoron Allah su guji kwadayi su tashi tsaye su hada kan al’ummar Najeriya.