Zakarun Turai: Manchester City ta kai ‘Final’ bayan cin Madrid 4-0
Yanzu Manchester City za ta kara da Inter Milan a wasan karshe, inda take fatan cika babban burin mai kungiyar, Sheikh Mansour, na cin kofin Gasar Zakarun Turai
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta tsallaka zuwa wasan karshe na Gasar Zakarun Turai bayan da ta yi wa Real Madrid dukan kawo wuka da ci 4-0.
A wasanni biyu da suka buga, Real Madrid wadda sau 14 tana daga kofin, ta kwashi kashinta da jimillar ci 5-1 a hannun Manchester City.
Karo na biyu ke nan da Manchester City take kaiwa wasan karshe na Gasar Zakarun Turai a cikin shekaru uku, inda a wannan karon za ta fuskanci Inter Milan a a birnin Santanbul na kasar Turkiyya a ranar 10 ga watan Yuni, 2023.
Manchester City na fatan cika babban burin mai kungiyar, Sheikh Mansour, na daga kofin Gasar Zakarun Turai, tun bayan da ya sayi kulob din a shekarar 2008 — amma Chelsea ta rika shan gabansu a kakannin wasa biyu da suka gabata.
A wasan City da Madrid na daren Laraba a filin wasa na Etihad, yunkurin Madrid na daga kofin a karo na 15 ya fara gamuwa da tarnaki ne bayan da Bernardo Silva na Manchester City ya zura mata kwallaye biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ana cikin haka kuma dan wasanta Eder Militao yi kuskuren zura mata na uku, kafin daga bisani Julian Alvarez ya cike na hudu.
A haka aka tafi hutun rabin lokaci tawagar Pep Guardiola na gaba da su da 4-0, kamar yadda Real Madrid ta yi musu a wasan kusa da na karshe a shekarar da ta gabata.
Kawo yanzu dai ba a doke Manchester City a gidanta a a wasanni 26 na Gasar Zakarun Turai.
Manchester City za ta kara da Inter Milan a matakin karshe inda take fatan cika babban burin mai kungiyar, Sheikh Mansour, na cin kofin Gasar Zakarun Turai, tun bayan da ya sayi kungiyar a shekarar 2008, amma Chelsea ta sha gabansu a kakannin wasa biyu da suka gabata.