Zakarun Turai: Wacce wainar za a toya tsakanin City da Madrid?
City ta zama ta uku daga Ingila da ta kai daf da karshe a kaka uku a jere.
Yau Talata ake shirin barje gumi tsakanin Real Madrid da Manchester City a wasan gab da na karshe na Gasar Kofin Zakarun Turai.
Wannan wasan dai an jima ana dakonsa don ganin yadda za ta kaya tsakanin manyan kungiyoyin biyu.
- Zaben Gwamnan Osun: Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Adeleke
- Hajj 2023: Kamfanonin jirage da NAHCON sun daidaita kan jigilar maniyyata
Duk da cewa Real Madrid na da tarihin lallasa Manchester City, amma kuma a yanzu wasu na ganin Cityn ta kara karfi musamman bayan zuwan Erling Haaland daga Borussia Dortmund da ya kange kungiyar daga shan kaye.
Tuni dai masu sharhi kan al’amuran wasanni suka fara tsokaci kan wannan haduwa ta yau wadda za a yi a gidan Madrid, wato filin wasa na Santiago Bernabeu.
Michael Brown, tsohon dan wasan Manchester City na ganin dole ne ’yan wasan na Guardiola su kaucewa kuskure a haduwar ta yau don kaucewa abin da ya faru a bara.
Ko a baran ma dai Real Madrid ce ta yi waje da City a irin wannan mataki bayan nasara da kwallaye 6 da 5 a jimillar haduwa biyun da suka yi.
Ana ganin dai Pep Guardiola zai iya amfani da salon zubin ‘yan wasan da ya yi a haduwarsu da Arsenal don kaucewa fuskantar matsala kwatankwacin wadda ya hadu da ita a haduwarsu ta bara.
Yadda kungiyoyin suka kawo wannan mataki
Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta yi waje da Chelsea da cin 4-0 gida da waje, tun kan nan ita ce ta fitar da Liverpool.
City kuwa ta yi nasarar doke Bayern Munich da cin 4-1 gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 ranar Laraba a Jamus a wasa na biyu a quarter finals.
Hakan ne ya sa Real Madrid mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla za ta kece raini da City, wadda ba ta taba lashe kofin ba.
Manchester City ta zama ta uku daga Ingila da ta kai daf da karshe a kaka uku a jere a Gasar Zakarun Turai, bayan Chelsea da Manchester United.
Kawo yanzu Erling Haaland na Manchester City ya ci kwallo 12 a Zakarun Turai, shi ne kan gaba a wannan kwazon,
Yayin da Vinicius Junior na Real Madrid ke da shida a raga kawo yanzu.