‘Zaki da bera’
Barkanmu da war haka Manyan Gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wani zaki da bera.’ Labarin na kunshe da yadda alheri ba ya taba zama kadan. A sha karatu lafiya. ‘Zaki da bera’ A wani daji akwai wani zaki wanda bai cika hulda da […]
Barkanmu da war haka Manyan Gobe, tare da fatan alheri kuma kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wani zaki da bera.’ Labarin na kunshe da yadda alheri ba ya taba zama kadan. A sha karatu lafiya.
‘Zaki da bera’
A wani daji akwai wani zaki wanda bai cika hulda da sauran namun daji ba. Wata rana sai barci ya dauke shi. Yana cikin barci mai nauyi sai ya ji wani abu ya fado kan hancinsa. Budar idonsa ke da wuya har ya kama abin da yake kan hancinsa. Ashe bera ne ya fada masa a kan hanci.
Sai ya ce sai ya kashe beran domin ai wannan rashin kunya ne. Bera sai ya fara karkarwa ya roki zaki a kan cewa ya yafe masa wata ran shi ma zai taimaka masa.
Abin sai ya ba zakin dariya a kan yaya za a yi bera ya taimake shi. Kawai dai sai ya bar bera.
Wata rana wani maharbi ya sanya tarko domin neman naman daji. Sai zaki ya fada a cikin tarkon. Sai ya fara ihu. Bera sai ya ji murya kamar na zakin. Sai ya biyo inda ake ihun. Nan take sai ya gano cewa zakin ne ya fada tarkon maharbi. Sai ya je ya katse igiyar tarkon da hakoransa. Zakin sai ya yi farin ciki da haka. Har ya fada wa bera cewa bai taba zaton zai taba taimaka masa ba.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a kan wannan labari.