Zaki ya kusa dawowa ya kori kuraye da dila daga gwamnatinsa – A’isha Buhari
Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari wadda har zuwa rubuta wannan rahoto take kasar Ingila don duba lafiyar mijinta Shugaba Buhari, ta yi wani shagube a kan al’amuran da suke faruwa a gwamnatinsa, inda, ta ce zaki ya yi kusan dawowa ya kori kuraye da dila daga gwamnatinsa. A’isha Buhari ta wallafa shaguben ne […]
Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari wadda har zuwa rubuta wannan rahoto take kasar Ingila don duba lafiyar mijinta Shugaba Buhari, ta yi wani shagube a kan al’amuran da suke faruwa a gwamnatinsa, inda, ta ce zaki ya yi kusan dawowa ya kori kuraye da dila daga gwamnatinsa. |
A’isha Buhari ta wallafa shaguben ne a shafinta na Facebook a ranar Litinin, inda ta yi amfani da abin da Sanata Shehu Sani na Jihar Kaduna ya rubuta yana habaici ga wadansu ’yan siyasa.
A makon jiya ne Hajiya A’isha Buhari ta sake komawa Landan domin duba Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya shafe sama da wata biyu a can yana jinya a karo na biyu a bana.
“Tuni aka daina yi wa babban zaki addu’a, har sai ya dawo sannan za ka ga suna rawar jikin kasancewa a sahun farko na ’yan kanzagi. A yanzu kuraye da dila na ta yi wa juna rada suna kokwanto ko Sarki Zaki zai dawo ko a’a. Sarkin dai barci yake a yanzu, kuma ba mai iya tabbatar da cewa zai tashi ko ba zai tashi ba. Amma fatan kuraye da dila shi ne kada ya tashi saboda su samu su zama sarakuna. A gefe guda sauran kananan dabbobi (talakawa) na ta addu’ar Sarki Zaki ya dawo domin ya ceci dawa daga miyagun namun daji irin su kuraye da diloli,” inji Shehu Sani.
A karin bayanin da Hajiya A’isha Buhari ta yi cewa ta yi: “Allah Ya amshi addu’ar kananan dabbobi (talakawa), nan ba da dadewa ba za a fatattaki kuraye da diloli daga dawa. Muna da yakini kan addu’a da goyon bayan kananan dabbobi. Allah Ya ja zamanin talakawa, Allah Ya ja zamanin Najeriya.”
Wadannan maganganu na Hajiya A’isha Buhari sun janyo sharhi da ka-ce na-ce sosai, musamman a shafukan sada zumunta da muhawara. Kuma ana ci gaba da mayar da martani a shafukan zumuntan inda wadansu ke jinjina wa kalaman nata, yayin da wadansu ke sukarta da cewa ta aibata ’yan Najeriya da ta kira su da dabbobi marasa karfi. Jam’iyyar PDP ta wallafa a shafinta na Tiwita cewa ’yan Najeriya su fahimci A’isha Buhari ta kira su da dabbobi marasa karfi, duk da cewa Sanata Shehu Sani ne ya fara yin amfani da kalmomin.
Akwai mutane da dama da suka ce ba su ga laifi a maganganun nata ba, domin a cewarsu kamar ‘adon magana ce.’
Kalamanta suna nuna batun da aka dade ana yi cewa ’yan ba-ni-na-iya da masu gogoriyon neman mulki a fadar gwamnatin Buharin suna hana ruwa gudu.