Zakir Naik ya lashe kyautar Sarki Faisal kan hidima ga Musulunci

Fitaccen malamin Musuluncin nan dan kasar Indiya Dokta Zakir Naik ne ya lashe lambar yabo ta Sarki Faisal ta duniya kan yi wa Musulunci hidima a bana Dokta Zakir Naik, wanda likita ne ya karbi kyautar ta Sarki Faisal ne a wani biki da aka gudanar a birnin Riyadh.Haifaffen Mumbai ta kasar Indiya mai shekara […]

Zakir Naik ya lashe kyautar Sarki Faisal kan hidima ga Musulunci
Zakir Naik ya lashe kyautar Sarki Faisal kan hidima ga Musulunci

Fitaccen malamin Musuluncin nan dan kasar Indiya Dokta Zakir Naik ne ya lashe lambar yabo ta Sarki Faisal ta duniya kan yi wa Musulunci hidima a bana

Dokta Zakir Naik, wanda likita ne ya karbi kyautar ta Sarki Faisal ne a wani biki da aka gudanar a birnin Riyadh.
Haifaffen Mumbai ta kasar Indiya mai shekara 49, ya yi fice wajen gudanar da wa’azi a kafafen talabijin, kuma yana daga cikin mutum biyar da suka karbi kyautar lambar zinare da satifiket da kuma Fam dubu 130 (kimanin Naira miliyan 39) daga Sarki Salman bin Abdul’aziz na Saudiyya a wani otel a ranar Litinin da ta gabata.
Dokta Naik wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Binicke ta Musulunci da ke Indiya, an karrama shi ne a matsayinsa na fitaccen mai yada Musulunci da ba Balarabe ba.
Ya kafa gidan talabijin na Peace Tb, wanda ake ganin shi ne kafar talabijin na duniya da ya kware wajen tattaunawa a tsakanin addinai da yake kaiwa ga masu harshen Ingilishi da suka haura miliyan 100, kamar yadda bayanin rayuwarsa da aka karanta ya nuna.
“Musulunci ne addinin da kadai zai iya kawo zaman lafiya ga dan Adam,” inji shi a wani faifan bidiyon da aka nuna kan tarihinsa a wajen bikin.
A jawabinsa na karbar kyautar a otel din Al Faisaliah da ke Riyad, Dokta Naik ya ce zai mika kudin ga gidan talabijin na Peace Tb.
’Ya’yan marigayi Sarki Faisal wanda ya rasu a 1975 ne suka kafa Gidauniyar Sarki Faisal a 1976.
Sauran wadanda suka samu lambobin yabon na bana sun hada da:
A Nazarin Addinin Musulunci Islamic, dan Saudiyya, Abdul’aziz bin Abdulrahman Kaki kan bincikensa game da kayayyakin tarihi na Musulmin Madina.
A harkar magani, dan Amurka, Jeffrey Iban Gordon, wanda bincikensa ya karfafa fahimtar wasu cututtuka kamar na kiba, wadda ke kara yaduwa a Saudiyya.
A bangaren kimiyya, Michael Gratzel na kasar Switzerland ne ya samu lambar kan bincikensa game da rana sai abokin gwamnisa Omar Mwannes Yaghi na Amurka kan bincikensa game sabon bincikensa kan yadda ake sarrafa karafuna.