Zakka tsari ne na gina al’umma – Hassan Dikko

Shugaban Majalisar Malamai ta dungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Idamatis Sunnah reshen Jihar Filato, Dokta Hassan Abubakar Dikko ya ce tsarin fitar da zakka da wadafi da ba da su ga wadanda shari’a ta ce aba da Musulunci ya zo da shi tsari ne na gina al’umma. Dokta Hassan Dikko ya bayyana haka ne lokacin […]

Zakka tsari ne na gina al’umma – Hassan Dikko

Dokta Hassan Abubakar DikkoShugaban Majalisar Malamai ta dungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Idamatis Sunnah reshen Jihar Filato, Dokta Hassan Abubakar Dikko ya ce tsarin fitar da zakka da wadafi da ba da su ga wadanda shari’a ta ce aba da Musulunci ya zo da shi tsari ne na gina al’umma.
Dokta Hassan Dikko ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a garin Shendam a ziyarar aiki da ya kai dananan hukumomin jihar 17 don saduwa da shugabannin dungiyar na yankunan tare da duba ayyukan dungiyar a makon jiya.
Ya ce da zakka da wakafi ne aka tafiyar da gwamnatocin Musulunci da suka gabata a duniya. “Kuma da dukiyar zakka da wadafi za mu iya rike dungiyar nan, har ma mu taimaka wa wasu dasashe. Amma dole sai mun fadakar da mutanenmu kan mahimmanci bayar da zakka da wadafi,” inji shi.
Dokta Dikko ya ce dungiyar ta yi tsari kan zakka da wadafi har ta rubuta littafi domin da ita za a tallafa wa fadirai da miskinai da marayu da marasa galihu.
Ya yi kira ga al’ummar Musulmi manoma da makiyaya da sauran masu dukiya su ba shirin zakka da wadafi goyan baya da hadin kai.
Dokta Dikko ya ce mutane da dama a yankin Shendam, sun ba da gagarumar gudunmawa wajen bundasa harkokin Musulunci. Kuma ya yaba wa shugabannin dungiyar na daramar hukumar kan dodarin da suke yi wajen gudanar da ayyukan dungiyar.
A jawabin shugaban majalisar malamai na daramar hukumar Malam Khalid Muhammad Inuwa ya ce rikice-rikicen da aka yi a Wase da Langtang kwanakin baya sun shafe su, domin adalla suna da rassa tara wadanda a yanzu babu wani Musulmi a wurare duk sun tashi. Don haka ya yi fatar a sanya su a addu’a.
A cikin tawagar Dokta Hassan Dikko akwai mataimakinsa na daya da na biyu, Hafiz Aliyu Abdulwahab da Ustaz Ibrahim Umar da shugaban gudanarwa na jihar Alhaji Isiyaka Dogara Isiyaka da mataimakinsa  na daya  Alhaji Garba Sule da sauransu.