Zakkar Fidda Kai ta fi kayan sallah da abincin sallah

Matasa na kin fitar da zakkar alhali suna rike da wayoyi masu tsada.

Zakkar Fidda Kai ta fi kayan sallah da abincin sallah

Malami a Jami’ar Jihar Gombe, Dokta Rasheed Abdulganiyu, ya ce muhimmancin fitar da Zakkar Fidda Kai ya fi na yin kayan sallah ko abincin sallah.

Da yake gabatar da jawabi a laccar Ramadan karo na farko da Hukumar Yada Labarai ta Jihar (GMC) ta shirya, malamin ya bayyana cewa ana fitar da zakkar ce kwana biyu ko uku kafin Sallah Karama.

Dokta Rasheed ya ce lokacin fitar da ita na wajibi shi ne kafin a je sallar idi, amma idan mutum ya jinkirta har aka dawo daga idi, to sadaka ya bayar ba Zakkar Fidda kai ba.

Ya bayyana cewa irin falala da ladar Zakkar Fidda Kai ce ta sa a wani kauli aka ce fitarwa da kuma bayar da ita ga mabukata ta fi mutum ya dinka kayan Sallah ko dafa abincin sallah a gidansa.

Matasa na kin fitar da Zakka

Malamin ya jawo hankalin matasa kan yadda wasunsu ke mallakar wayoyin hannu masu tsada, amma suke kin fitar da zakkar, ga shi babu wani wanda ke fitar musu da ita.

Ya bayyana cewa rashin fitar da Zakkar asara ce a gare su, a don haka a shawarce su da su kiyaye wurin tabbatar da ganin sun fitar.

Hakazalika ya jaddada muhimmancin manyan mata masu aure su koyi yadda ake fitar da zakkar, saboda idan mazajensu ba sa nan, sai su su fitar.

Daga nan sai ya karfafi mutane da cewa su guji son zuciyar da za ta sa mutum shinkafa yake ci a gidansa, amma idan ya tashi fitar da zakkar sai ya bayar da dawa ko masara.

Sai dai ya ce yin hakan ba laifi ba ne, amma mutum ya rage wa kansa lada a wajen Allah.