Zaman lafiya ke sa karuwar ’yan gudun hijira a yankin Tilde – Hakimi
Sarkin Tilden Fulani kuma Hakimin Tilde da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Aliyu Muhammad Tukur ya ce saboda zaman lafiyar da suke da shi a yankin ya sa suke samun ’yan gudun hijira daga wuraren da ake fama da rikice-rikice a jihohin Filato da Kaduna. Hakimin ya bayyana haka ne a lokacin […]
Sarkin Tilden Fulani kuma Hakimin Tilde da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Aliyu Muhammad Tukur ya ce saboda zaman lafiyar da suke da shi a yankin ya sa suke samun ’yan gudun hijira daga wuraren da ake fama da rikice-rikice a jihohin Filato da Kaduna.
Hakimin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a fadarsa, inda ya ce har zuwa yanzu suna karbar ’yan gudun hijira a yankin. “Kuma duk ’yan gudun hijirar da suka zo muna karbarsu mu rubuta wa karamar hukumar cewa ga yawan ’yan gudun hijirar da suka zo, ita kuma ta rubuta wa gwamnatin Jihar Bauchi a taimaka musu daidai gwargwado,” inji shi.
Ya ce a kowanne lokaci suna gaya wa irin wadannan ’yan gudun hijira cewa su zauna lafiya da mutanen da suka tarar a yankin. Don haka ne tunda suke samun ’yan gudun hijira a yankin babu wata fitina da suka taba samu daga gare su.
Hakimin ya ce akwai zaman lafiya a yankin kuma akwai makarantun boko da na addini, sannan suna noma da kiwon dabbobi kamar shanu da tumaki da awaki da kuma kaji, wanda hakan ya sa mutane daga ko’ina suke sha’awar dawowa yankin da zama.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da na kasa baki daya su zauna lafiya a ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya kawo zaman lafiya a Najeriya.