Zaman Lafiya: Ya zama wajibi gwamnati ta kula da matasa – Shaikh Ahmad Gumi
A makon da ya gabata ne rikici ya barke a Jihar Kaduna, inda aka samu asarar rayuka da na dukiyoyi. Aminiya ta tattauna da babban malamin Musulunci a Kaduna, Dokta Ahmad Gumi, inda ya shawarci gwamnati a kan ta mayar da hankali ga matasa ta hanyar samar masu da sana’o’i tare da taimaka masu wajen […]
Sheik Ahmad Gumi
A makon da ya gabata ne rikici ya barke a Jihar Kaduna, inda aka samu asarar rayuka da na dukiyoyi. Aminiya ta tattauna da babban malamin Musulunci a Kaduna, Dokta Ahmad Gumi, inda ya shawarci gwamnati a kan ta mayar da hankali ga matasa ta hanyar samar masu da sana’o’i tare da taimaka masu wajen ci gaba da karatunsu a matsayin matakin magance irin rigingimun da ke faruwa cikin al’umma.
Wane jan hankali za ka yi wa mutane a kan zaman lafiya?
Shi dai zaman lafiya abu ne da addinin Musulunci ya kwadaitar da shi. Manzon Allah ya kwadaitar da sahabbansa a kan son zaman lafiya. Kuma sai da zaman lafiya nan ake samun ci gaba.
Hatta addininka ma ba ka samun natsuwa ka yi shi sai da zaman lafiya. Kuma an ce zaman lafiya a tsakaninsu da kuma a tsakaninsu da wadanda ba Musulmi ba. Kuma an ce duk mutumin da ya kashe wata rai da aka yi alkawarin zaman lafiya da ita, to wannan bai jin kamshin aljanna.
Kun ga ke nan zaman lafiyar har a irin wannan zamani namu na yanzu ya zama wajibi, tun da alkawari aka yi na dinkin duniya gaba daya. Cewa mutane su zauna lafiya, idan suna da wata matsala su kawo ta tebori a duba ta. Wannan ya sa babu wani dalili da zai sa mutum ya dauki makami ya kai wa wani hari.
Wane jan hankali Malam zai yi kan masu yada jita-jita?
Masu yada jita-jita su sani cewa addinin Musulunci ya hana yin hakan. Allah Ya ce idan wani abu ya zo koda na aminci ne, to kada a yada shi balle kuma wanda ba na aminci ba. Allah Ya ce idan wani abu na tsoro ya zo, ko na aminci sai su je suna ta yadawa, to an hana yadawa. Abin da ake yi shi ne mayar wa da shugabanni ake yi. Komai ya fito akwai yadda ake yi idan na tsoro ne sai a fada wa soja da ’yan sanda, idan kuma na rashin lafiya ne ga likitoci, idan kuma na siyasa ne ga shugabannin siyasa.
Idan kuma abu na addini ne ga malaman addini. Komai dai na da nasa fanni, babu kyau mutane su rika yada jita-jita. Kamata ya yi su sanar da shugabani, su kuma sai su duba lamarin su yanke hukunci.
Wane jan hankali za ka yi ga matasa, wadanda akasari suke haddasa rikici cikin al’umma?
Ai gaskiya abin wani lokaci ba wai maganar addini ba ce ko kabilanci. Wani lokaci rashin aikin yi da kuma wasu abubuwa na shaye-shaye da kuma son a samu irin wadannan tarzoma domin a yi wa mutane sata. Duk yawanci shi ne ba wai wata maganar addini ba ce. Saboda haka muna kira ga iyaye da gwamnati da duk shugabanni da a kula da matasa. Koda an tarbiyyantar da su, a koyar da su ilimi tare da ba su aikin yi. Idan aka yi haka in sha Allahu za a samu saukin irin wadannan abubuwa.
Su iyaye fa, wane kira za ka yi gare su a kan tarbiyyar ’ya’yansu?
Su ma iyaye an ce ita ce tun yana danye ake tankwasa shi. Tun yara na kanana ya kamata sun kula da su amma mutane an bar tarbiyya har sun tashi daga shaye-shaye sai iskanci cikin gari. To idan yaro ya kosa ya balaga, yaushe za ka iya kuma tankwasa shi. Amma dai duk da haka akwai bukatar hukuma ta mayar da hankali zuwa ga matasa. Lallai a samar masu aiki kuma a samar masu hanyoyin ci gaba da karatunsu.