Zaman lafiyar da aka samu a gwamnatin Buhari ya fi na gwamnatocin baya – Shariff Usmaniyya

Wani shugaban al’umma da ke Kaduna Alhaji Sharrif Abubakar Usmaniya ya ce zaman lafiyar da aka samu a kasar nan a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya fi na gwamnatocin baya. Alhaji Sharrif Usmaniyya ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a lokacin da yake mai da martani ga kalaman tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo […]

Zaman lafiyar da aka samu a gwamnatin Buhari ya fi na gwamnatocin baya – Shariff Usmaniyya
Zaman lafiyar da aka samu a gwamnatin Buhari ya fi na gwamnatocin baya – Shariff Usmaniyya

Wani shugaban al’umma da ke Kaduna Alhaji Sharrif Abubakar Usmaniya ya ce zaman lafiyar da aka samu a kasar nan a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya fi na gwamnatocin baya.

Alhaji Sharrif Usmaniyya ya bayyana haka ne a zantawarsa da Aminiya a lokacin da yake mai da martani ga kalaman tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda ya ce gwamnatin Buhari ta gaza.

Alhaji Shariff ya bayyana takaicinsa kan kalaman na Obasanjo wanda ya bayyana su da soke-burutsu.

Ya ce ya kamata a rika yi wa wannan gwamnati adalci a shekara ukun da ta yi a karagar mulki. A cewarsa bai kamata gwamnatin da ta tarar da an ruguza tattalin arzikin kasa da rashin tsaro da ya samo asali tun zamanin mulkin Obasanjo hade da dorewar cin hanci da rashawa a ce ta gyara komai nan take ba.

“Ya kamata ’yan Najeriya su yi karatun ta-natsu tare da waiwayen irin bakar ukubar da suka dade suna fama da ita da wannan gwamnati ke kokarin gyarawa. A rana guda akan iya rusa kasa amma gina ta sai an bi sannu a hankali. Ko yanzu zaman lafiyar da aka samu a wannan gwamnati ya fi na gwamnatocin baya,” inji shi. 

Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta tashi haikan wajen magance talauci da samar da ilimi cikin sauki ga ’ya’yan talakawa da nufin rage ta’addanci domin a samu dauwamammen zaman lafiya a kasa.

Ya ce dorewar zaman lafiya ba zai samu ba a hali na rashin ilimi da talauci da rashin aikin yi, musamman ga matasa.