‘Zaman lafiyar da ake cewa an samu a Kudancin Taraba siyasa ce’
Al’ummar da rikicin addini da kabilanci ya tilasta wa kaurace wa gidajensu a gururuwan Wukari da Ibbi da Gareji da sauransu a Kudancin Jihar Taraba sun nuna shakku cewa zaman lafiyar da aka ce an samu yanzu a yankin an yi ne don cimma wani buri na siyasa. Wannan na zuwa ne duk da tabbacin […]
Al’ummar da rikicin addini da kabilanci ya tilasta wa kaurace wa gidajensu a gururuwan Wukari da Ibbi da Gareji da sauransu a Kudancin Jihar Taraba sun nuna shakku cewa zaman lafiyar da aka ce an samu yanzu a yankin an yi ne don cimma wani buri na siyasa.
Wannan na zuwa ne duk da tabbacin da manyan ’yan siyasar yankin suka bayar cewa za su maida hankalin wajen tabbatar da dauwamamen zaman lafiya a daukacin yankin wanda ya yi kaurin suna kan fadace-fadacen da suke da alaka da addini da kabilanci.
A lokacin da yake jawabi a wani gangamin siyasa a garin Wukari dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar SDP Mista Dabid Kente ya bayar da tabbacin cewa in ya zama Gwamnan Jihar abu na farko da zai yi shi ne maido da zaman lafiya a yankinn Kudancin Taraba.
Mista Dabid Kente ya ce zai hada kawunan kabilun Jukun da Tibi da Hausawa da Fulani a yankin Wukari don samun tabbatacen zaman lafiya a yankin.
Ya ce yana da muhimmanci jama’a su fahimci amfanin zaman lafiya domin shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.
Ya nuna takaicin irin asarar rayuka da dukiya da aka yi a sanadiyyar fadace-fadacen da suka auku a yankin.
Mista Dabid Kente ya bayar da tabbacin cewa in ya zama gwamna zai rungumi kowa da kowa a daukacin jihar don samun zaman lafiya da cigaba mai dorewa a jihar.
Ya kuma yi alkawarin sake ginawa wadanda aka konawa gidajensu a lokacin rigingimun tare da basu taimakon kudi don gudanar da sana’o’i.
Ya ce wasu yan siyasa da suka zo yankin basu ziyarci inda aka tsugunar da yan gudun hira dake garin na Wukari ba.
Mista Kente ya ce saboda bukatarsa ta neman hanyoyin kawo karshen tashin hankali a yankin ya sa ya ziyarci inda aka tsugunar da ’yan gudun hijira da kuma wuraren da aka kone a lokacin fadan.
Duk da irin wadannan kalamai da ’yan siyasar yanki ke yi wasu wadanda bala’in fadace- fadacen ya shafa a sun nuna tsoron cewa ’yan siyasar na yin wadannan kalamai ne yanzu don neman kuri’a daga mazauna yankin.
daya daga cikin wadannan mutane Alhaji Ibrahim Lawal wanda ya ce shi dan kabilar Jukun ne amma an kashe iyalansa an kone gidansa a lokacin fadan, ya ce yanzu haka yana gudun hijira a garin Jalingo saboda haka yana fata cewa irin wadannan kalamai da ’yan siyasa ke yi na neman kawo karshen fadace-fadace a yankin da gaske suke yi.
Ya ce dama rigingimun da suke aukuwa a yanki kitsa su aka yi don cimma wata manufa ta siyasa kawai.