Zaman Mutum (2)

Mutumin da ya kula da kansa kadai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya fadi maganar da take daidai ba zai yarda ba. Wawa bai kula ba, ko ya fahimci abu, ko bai fahimta ba. Abin da yake so ya yi kadai, shi ne ya nuna kuzarinsa. Zunubi da kunya a tattare suke. Idan […]

Zaman Mutum (2)
Zaman Mutum (2)

Mutumin da ya kula da kansa kadai ba ya jituwa da kowa, ko wani ya fadi maganar da take daidai ba zai yarda ba. Wawa bai kula ba, ko ya fahimci abu, ko bai fahimta ba. Abin da yake so ya yi kadai, shi ne ya nuna kuzarinsa. Zunubi da kunya a tattare suke. Idan ka yar da mutuncinka za ka sha ba’a a maimakonsa. Harshen dan Adam yana iya zama shi ne asalin hikima mai zurfi kamar teku, sabo kamar ruwan rafi mai gudu. Ba daidai ba ne a yi wa mugun mutum alheri, sa’an nan a ki yi wa marar laifi adalci. Sa’ar da wawa ya fara jayayya, yana neman duka ne. Sa’ar da wawa ya yi magana yana lalatar da kansa ne, maganarsa tarko ce da ita ake kama shi. Dandanar jita-jita dadi gare ta, mukan kosa mu hadiye ta. Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa. Sunan Ubangiji kamar kakkarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya. Attajirai suna zaton dukiyarsu ita ce za ta kiyaye su kamar katangu masu tsayi da suke kewaye da birni. Ba wanda za a girmama sai mai tawali’u, mutum mai girman kai kuwa yana kan hanyar hallaka. Ka saurara kafin ka amsa, idan kuwa ba ka yi ba, ka zama dakiki mai ban kunya. Sa zuciya ga rai yakan taimaki mutum sa’ar da yake ciwo, amma idan ya karaya, to, tasa ta kare. Mutane masu basira a koyaushe suna da himma, a shirye kuma suke domin su koya. Kana so ka sadu da babban mutum? Ka kai masa kyauta, za ka gan shi a sawwake. Wanda ya fara mai da magana a majalisa yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai abokin shari’arsa ya mai da tasa maganar tukuna. Idan mutum biyu karfafa suna jayayya da juna a gaban shari’a, kuri’a a asirce kadai take iya daidaita tsakaninsu. Dan uwan da ya ji haushinka zai gagare ka, idan ka yi fada da shi zai rufe maka kofarsa. Bisa ga sakamakon furucinka haka za ka rayu. Abin da ka fada ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karbi sakamakon maganarka. Idan ka samu mace ka samu abu mai kyau, wannan alheri ne wanda Ubangiji Ya yi maka. Matalauci yakan yi roko da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas. Wadansu abokai ba su sukan dore ba, amma wadansu abokai sun fi ’yan uwa aminci.

Gara mutum ya zama matalauci amma mai aminci, da a ce ya zama makaryaci, wawa. Yin dokin da ba ilimi ba ya da amfani, rashin hakuri kuma zai jawo maka wahala. Wadansu mutane sukan lalatar da kansu ta wurin ayyukansu na jahilci, sa’an nan su sa wa Ubangiji laifi. Attajirai sukan samu sababbin abokai a koyaushe, amma matalauta ba zu su iya rikon ’yan kadan da suke da su ba. Idan ka fadi karya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kubuta ba. Kowa na kokari ya samu farin jini wurin manyan mutane, kowa na so a ce shi abokin mutumin nan ne, mai yawan alheri. ’Yan uwan matalauci ba su bukatarsa, ba abin mamaki ba ne ya rasa abokai. Komai kokarin da zai yi ba zai samu ko daya ba. Ka yi wa kanka gatanci, ka koyi dukan abin da kake iyawa, sa’an nan ka tuna da abin da ka koya, za ka arzuta. Ba wanda zai fadi karya a majalisa ya rasa shan hukunci, makaryaci, tasa ta kare. Ko kusa wawaye ba za su yi zaman jin dadi ba, haka nan kuma bayi ba za su yi mulki a kan iyayen gijinsu ba. Mutum mai hankali yake danne fushinsa. Lokacin da wani ya cuce ka, abin kirki ne, ka yi kamar ba ka kula da shi ba. Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne. Dakikin da yana jawo wa mahaifinsa lalacewa, mace mai mita tana kama da diddigar ruwa. Mutum na iya cin gadon gida da kudi daga wurin iyayensa, amma Ubangiji ne kadai Yake ba shi mace mai hankali. Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa. Ka kiyaye umarni za ka rayu, in ka ki bin su kuwa za ka mutu. Sa’ar da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai saka maka. Ka yi wa ’ya’yanka tarbiyya tun suna kanana yadda za su iya koyo. Idan ba ka yi haka ba, ka taimaka wajen lalacewarsu ke nan. Idan mutum mai zafin rai ne, kyale shi ya sha sakamakonsa. Idan ka fisshe shi daga cikin wahala sau daya, sai ka sake yi. Ka saurari shawara, ka yarda ka koya, wata rana za ka zama mai hikima. Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata. Abin kunya ne mutum ya zama mai hadama, matalauci kuma ya fi makaryaci. Ka yi tsoron Ubangiji za ka yi tsawon rai, ka kuma samu biyan bukata, ba abin da zai cuce ka. Wadansu mutane sun cika lalaci, ko abincinsu ba su iya taunawa. Za a hukunta mai fariya saboda ya zama ishara ga mutanen da ba su san komai ba, mutum mai hikima yakan koya sa’ar da aka tsawata masa. Sai marar kunya, marar mutunci yake wulakanta mahaifinsa, ko ya kori mahaifiyarsa daga gidansa. Dana idan ka bar yin nazari za ka manta da abin da ka riga ka koya. Ba gaskiya ga mashaidin da ya yi niyyar cutar wani. Mugaye suna kaunar yin mugunta. Wawa mai fariya hakika zai sha duka.

Karin Magana 18,19