Zamani ya shafi aikin Sa’i – Sa’in Kano
Hakimin Makoda kuma Sa’in Kano, Dokta Wada Waziri ya ce sarautar Sa’i ta na da muhimmanci idan aka dubi tarihinta, musamman a tsarin sarautar gargajiya irin ta kasar Hausa. Ya yi wannan bayani ne da ma wasu batutuwan cikin zantawar su da wakilinmu dangane da sarautar ta Sa’i. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: […]
Hakimin Makoda kuma Sa’in Kano, Dokta Wada Waziri ya ce sarautar Sa’i ta na da muhimmanci idan aka dubi tarihinta, musamman a tsarin sarautar gargajiya irin ta kasar Hausa. Ya yi wannan bayani ne da ma wasu batutuwan cikin zantawar su da wakilinmu dangane da sarautar ta Sa’i. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ranka ya dade masu karatu za su so jin yadda Sarautar Sa’i take da kuma aikace-aikacenta ?
Sa’in Kano: Sarautar Sa’i ta na da asali mai kyau da daraja kuma tun a zamanin Shehu Usman dan Fodio ake yenta, sai dai tarihinta gajere ne a Jihar Kano, saboda a zamanin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Abdullahi Bayero watau mahaifi ga marigayi Alhaji Ado Bayero aka fara yenta, inda aka fara nada kanen marigayi Malam Aminu Kano mai suna Mustapha Yusuf a matsayin Sa’in Kano na farko. Sannan aka nada Malam Lawan Tudun Wada kana kuma aka nada ni lokacin marigayi Alhaji Ado Bayero, Allah Ya gafarta masa da sauran musulmin da suka riga mu gidan gaskiya a duk inda suke a fadin duniya.
Babban aikin Sa’i da kuma yadda sarautar take shi ne karbar zakka da raba ta ga wadanda suka cancanci a ba su ita, wannan shine aikin Sa’i kuma sarauta ce mai muhimmanci saboda muhimmancin aikin mai wannan sarauta a duk inda yake.
Aminiya: Ko akwai bambanci tsakanin aikin Sa’i a wancan zamani na Daular Shehu Usman dan Fodio da wannan lokaci da muke ciki?
Sa’in Kano: Akwai bambance-bambance tsakanin aikin Sa’i a wancan zamani da kuma yanzu, ka ga dai yanzu akwai hukumomi da aka kakkafa domin karba da raba ita kanta zakkar wadanda ake kira hukumomin zakka da hubusi. Sannan duk wasu ayyuka na tattara zakka da rarraba ta ga al’umma suna karkashin wannan hukuma ta zakka kuma suna yin aiki mai gamsarwa babu wata matsala. Don haka zamani ya kawo canje-canje kuma al’amura suna tafiya da zamani ganin yadda a kullum wasu sabbin manufofi ake bijirowa da su saboda wannan juyi na zamani.
Aminiya: Sarakunan gargajiya su na bada guummawa wajen cimma nasarorin wasu shirye-shiryen gwamnati, ya ya kake kallon wannan al’amari?
Sa’in Kano: Babu shakka sarakunan gargajiya suna taimakawa matuka wajen cimma nasarorn shirye-shiryen gwamnati, sannan sun kasance iyayen kasa saboda martabar da Allah ya ba su tun lokaci mai tsawo. Don haka ina gamsuwa bisa yadda kowa ya yarda cewa sarautar gargajiya tana da amfani da kuma muhimmanci a kowace kasa ta duniya, saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa da kuma kaunar juna.
Yanzu idan ka dubi irin ayyukan sarakunan gargajiya zaka ga cewa suna kokari sosai kuma ta fannoni daban-daban wanda lokaci ba zai bari a fayyace komai duka ba, kuma Alhamdulillahi suna da matukar amfani ga zamantakewar al’umma walau a birane ko yankunan karkara.
Aminiya: Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya fara rangadin zagayen kasa, sai kuma aka dakatar, ko me ya kawo haka?
Sa’in Kano: Gaskiya ne cewa Mai Martaba Sarki ya fara zagayen kasa kuma sai aka dakatar, amma ina so kowa ya sani cewa akwai abubuwa masu tarin yawa da suka yi wa sarki yawa, kuma yana samun gayyata daga gurare daban-daban a cikin gida da wajen kasar nan domin gudanar da wasu hidimomi da suka shafi tattalin arzikin duniya. Don haka ba ya samun lokaci mai yawa da zai cigaba da wancan zagaye, amma na san abin yana zuciyarsa kuma sarki mai son ganawa da al’umarsa ne, kuma mutum ne mai son haduwa da talakawansa domin jin matsalolinsu. Don haka nasan wata rana za a cigaba da wannan zagaye kuma mai martaba sarkin kano zai so ace ya gaisa da al’umarsa musamman ta irin wannan hanya watau rangadi, wanda ta haka ne zai ziyarci talakawa har yankunansu, sannan a waje guda su ma talakawan jihar Kano suna son gaida sarkinsu domin duk wanda ya ga yadda aka ziyarci wasu gundumomi zai yarda cewa sarki Muhammadu Sanusi na II shugaba ne mai son al’umarsa babu kyama ko musgunawa.
Aminiya: Wasu na kiraye-kirayen cewa a baiwa sarakunan gargajiya wani hurumi a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, me zaka ce kan wannan?
Sa’in Kano: Wannan babban al’amari ne, amma ina so ma su waccan magana su gane cewa ko yanzu sarakunan gargajiya suna da abubuwan yi a kasar nan, domin su ne iyayen kasa kuma duk abin da za a yi sai an sanya su a ciki, sannan sune suke bada gagarumar gudummawa wajen cimma nasarar wasu shirye-shirye. Don haka ina so kowa ya sani cewa har yanzu sarakunan gargajiya suna da ayyukan yi kuma suna nan a matsayinsu na iyayen kasa. Babu wata gwamnati da ba ta tafiya da su kuma ana aiki tare bisa mutunta juna da kokarin ciyar da kasa gaba a koda yaushe. Ina kuma godiya ga al’uma bisa biyayya da goyon baya da suke baiwa sarakunan gargajiya tare da fatan cewa za a cigaba da zama lafiya da kaunar juna a fadin kasa baki daya.