Zamanka lafiya da Buhari ka bi doka – Ciroman Daura
A makon jiya ne Aminiya ta samu ganawa da Ciroman Daura Alhaji Zakari Abubakar wanda suka yi makarantar elementare dtare a Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa a yadda ya san Buhari ba su sanya ran zai fifita Daura ko mutanenta a matsayinsa na Shugaban kasa: kuma zamanka lafiya da shi ka bi doka. […]

A makon jiya ne Aminiya ta samu ganawa da Ciroman Daura Alhaji Zakari Abubakar wanda suka yi makarantar elementare dtare a Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa a yadda ya san Buhari ba su sanya ran zai fifita Daura ko mutanenta a matsayinsa na Shugaban kasa: kuma zamanka lafiya da shi ka bi doka. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ranka ya dade ko za mu fara da ji cikakken sunanka?
Ciroma: Eh, ni ne Ciroman Daura, sunana Zakari Abubakar.
Aminiya: Kuma kun yi makaranta elemantare ke nan tare da shi Janar Muhammadu Buhari?
Ciroma: kwarai kuwa, mun yi makaranta da shi a 1951 a lokacin an yi wa yayansa Malam Dauda canjin wuri aiki, lokacin shi ne hedimasta aka tura shi zuwa Mai’aduwa. Mu kuma lokacin mu ne ’yan elemantare sai ya zo muka hadu a ajinmu tare da shi muka gama. Farko daga nan Daura ya fara da aka yi wa yayan nasa canjin wurin aiki suka tafi tare, to a nan kuma muka yi makarantar tare har muka gama tare. Kuma mun riga mun saba kwarai da gaske ko an tashi daga makaranta nakan zo wurinsu mu yi ta hira mu rika wasanninmu na yara.
Aminiya: Ban da shi da kai, su wa su wane ne suka saura a cikin wadanda kuka yi makaranta tare?
Ciroma: Wasu da yawa sun rasu a can Mai’aduwa yawancinsu sun rasu. Wadanda zan iya tunawa akwai Sanda Shu’aibu, akwai Ali Jikan Goje, akwai Ibra (Ibrahim) Sarkin Noma shi yana nan da ransa, akwai kuma Ibra (Ibrahim) baure, shi ma yana nan da ransa. Wadannan biyun na san suna da rai, amma sauran kusan duk sun rasu. A mata kuma akwai wata Nana Hamza ita ma tana da rai, sauran duk sun rasu.
Aminiya: Ashe ajin naku har akwai ’yan mata?
Ciroma: Akwai ’yan mata amma su shida ne a lokacin. Mu 36 ne a lokacin, amma sai ya zamanto guda shida mata, mu kuma maza mu 30.
Aminiya: Kamar ga shi ya zo yana ban kwana kafin ya je a sakar masa kura ( Najeriya) na san kila kun hadu ko za ku hadu, wace shawara za a ba shi a daidai wannan lokaci?
Ciroma: To, maganar shawara a tsakanina da Janar Buhari ba yanzu aka fara ta ba. Domin duk yadda ya kai, tunda Allah Ya yi shi, shi mutum ne mai amana. Haka Allah Ya yi shi. Don duk lokacin da na je ko baki ya yi sai ya ce su jira abokinsa ne, ya ce dan ajinmu ne a Mai’aduwa kaza-kaza-kaza. Kuma in na je muna hira da shi sosai, kuma ya san ina da ra’ayi na rikau kwarai da gaske. A tafiyar da ya yi ta yi ta siyasa, musamman shekarar da ya fara shiga zabe aka zo ga shi, ga shi, kamar zai ci, kamar shi ya ci, aka zo aka ce daga baya abubuwa aka ce ba shi ba ne. Hankalina ya yi muguwar tashi, na je na same shi, sai na iske shi da jama’a ana ta tadi ana ta hira. Sai na ce Janar ina so in gan ka sai muka kebe ni da shi, muka koma ofishinsa a cikin gidansa. Na ce Janar wane irin mutum ne kai? Ya ce me ka gani? Na ce yanzu wannan faduwar da muka yi ta zabe, mu mun kasa barci, raina a bace, barci ma ba na iya yi, amma kai ga ka sai dariya kake yi babu abin da ya dame ka? Sai ya ce in kwantar da hankalina don Allah in zauna sosai.
Ya ce babu abin da ya dame ni da sha’anin zabe. Ni abin da na dauka ainihin jama’ar Najeriya aka yi wa asara, ina so in bada gudunmawar da nake ganin zan iya badawa a Najeriya. To, in an hana ni, Allah ne bai bada ba, saboda haka ganin da nake yi ba wani aka yi wa asara ba, jama’a aka yi wa asara. Ya ce kuma da ka ga ban damu ba ana ta hira ana ta raha, ba ka ga damuwa ba a fuskata ba, kai kuwa ga shi saboda ni kana da ta damuwa har ka ce ka kasa barci. Na ce, eh. Ya ce ai ni babu abin da ya dame ni a duniyar nan, in ban da abu uku. Sai na ce wadanne ne? Ya ce na daya idan lokacin ibadata ya yi, ko me nake yi in bari in tafi in je in yi ibadata. Na biyu lokacin cin abincina in ya yi, ko me nake in bari in je in ci abinci a wannan lokaci. Na uku shi ne lokacin barcina in ya yi, duk abin da nake
in lokacin ya yi in je in kwanta. Ya ce ka ga wadannan ukun su kadai suka dame ni. Amma harkar duniya babu abin da yake hana ni barci. Shi ke nan sai na ce, alhamdulillahi da na samu wannan halin ni ma da na ji dadi.
Aminiya: To yaya ka ji a wannan karo da yake na daya, na biyu, na uku, duk ba a samun nasara, a wannan karo na hudu an zo an yi nasara?
Ciroma: Wato da farko lokacin da na ji, sai da na yi kuka. Na kasa rike hawaye sai da na yi kuka saboda jin dadi. Kuma na rasa inda zan sa kaina, na rika jin dadi wanda ban taba ji ba, saboda wata bukata ce da muke da ita a duniyar nan. Wato ina da kishi, ko da ba a nan Allah Ya yi shi ba, saboda halinsa dole zan so shi. Sai ga shi kuma Allah Ya yi shi tare muka tashi, tare muka yi komai, saboda haka sai abin ya kara shigar min rai. Saboda haka har kuka sai da na yi don murna. Kuma lokacin da ya zo nan Mai martaba Sarkin Daura ya ce mu je gaba daya mu yi masa murna. Da muka je ni ne mutum na farko da na fara zuwa muka gaisa, bayan sun gaisa da Sarki suna zaune. Sai Mai martaba ya ce, to, wannan dai ba ya bukatar gabatarwa Mai girma. Sai (Buhari) ya ce Ciroma! Ya ce ai bari in gaya maka Mai martaba abin da Ciroma ya zo ya yi min wani lokaci, bayan an kada mu a zabe.
Sai ya maimaita wannan magana da na fadi, wato a zuwansa na kwanan nan ba a yi mako biyu ba. Aka yi ta dariya, to amma ban maida amsa ba, na ce ai gaskiya ce. Wato shi ne abin nake mamaki da bai manta ba, duk abin da aka yi sai da ya tuna. Kuma duk abin da ya faru, ya dauka mu nasa ne, idan wani abu ya faru, idan ya shafe shi ne a kashin kansa, sai ka ga ya aiko min, a ce Buhari ya ce kaza-kaza. Wato duk wani abu wanda ka sani ya dauka kamar dan uwa ne, duk abin da ka sani na al’ada wanda ake yi da ’yan uwa ya dauka mu ’yan uwansa ne alhamdulillahi, muna ciki babu abin da za mu ce, sai godiya, shi mutum ne mai bada mutunci. In kuma wani abu ne wanda ko wani wuri za a je in dai gayya tasu ce, to, dole sai na je, kuma shi da kansa yakan taso ya zo wurina.
Wani lokaci ya zo nan gidana ka san shi Janar Buhari ba ya bakunta, ba a sabawa da shi, aka ce ai Janar ne ga shi can gidan Ciroma, kafin ka ce me, an cika gidan nan tam. Aka tsare, ’yan sanda suka hana mutane shiga da kyar wasu suka samu suka shiga, amma duk da haka, sai da masu daukar hoto, suka shiga suka dauki hotonmu a wancan lokacin, har yanzu hoton yana nan. Saboda haka shi mutum ne mai amana, mutum in kai nasa ne, to, nasa ne, wannan abu yana ba ni sha’awa kuma da irin halinsa na rikau. Ni da kaina ina da hali na rikau na son aikata gaskiya a kan kowane al’amari na duniya, amma sai in ga na yi, na yi, in tadda Buhari amma ina ba zai yiwu ba! Saboda kowa da yadda Allah Ya yi shi, abin da ya ce eh, eh ne, ba zai canja ba. Shi abin duniya ba wani abu ba ne bai rufe masa ido ba. Kuma ba ya yarda ka ce za ka yi amfani da Janar Buhari ka cimma wata bukata taka ba wadda za ta taimaki jama’a ba. Ko dansa ko shi ya haife ka ba za ka aikata wani abu na laifi ya goya maka baya ba. Shi al’adarsa wanda duk ke tare da shi ya rike doka.
Aminiya: Kamar yanzu da ga shi ya zama Shugaban kasa, ku kuma ku ne shugabannin al’umma a nan, akwai kamar wani abu d kuke sa ran ya yi wa Najeriya ko ya yi wa ita kanta Daura?
Ciroma: Wato abin da zan ce na farko dai na tabbata zai yi wa Najeriya wani abu. Dalili duk wani abu da ake cewa na kuskure ne, ko zalunci ne ko rashin gaskiya ne, ko son kai ne to ba za ka samu Janar a cikin ko daya ba. Kuma balle a ce shi ne babba a cikin al’amari. Saboda haka duk abin da zai taimaki jama’a kowace irin wahala za a sha, to zai tsaya a yi. Ni kum na tabbata a yadda kasar nan take in an tsare gaskiya abubuwa na gwamnati za a yi su yadda ya kamata, to in Allah Ya yarda za a ga bambanci. Kuma watakila za ku yarda da ni cewa, mu muna ganin tun daga lokacin da aka ce ya ci zaben nan mun fara samun dan sauki. Kamar mutum bai da lafiya ne, bai sha magani ba, amma ya rika jin ya fara samun sauki, yanzu haka Najeriya take. Yanzu abubuwa da yawa muna gani suna canjawa kadan-kadan, kuma kowa yana (jan) damara. Idan wani mutum ma’aikacin gwamnati ne in azzalumi ne shi wanda ya yi minista an san shi yana takama da wane ne da wane ne tun daga yanzu ya fara shiga taitayinsa. Saboda haka wannan ra’ayi na Janar Buhari shi muke fata ya tabbata ya dore Najeriya ta fita daga cikin kangi. Domin shekara takwas ke nan yana wahala yana ta waye wa mutane kai cewa idan kun zo zabe ku rabu da maganar kudi ko wani abu ku zabi cancanta, wanda duk kuka san zai yi muku aiki ku zabe shi. Aka ce kudi ake badawa ya ce to, ba za mu hana ku ku karbi kudi ba, tunda kudin kila naku ne aka dauko, amma rudun banza ne ko kun amsa ku zabi cancanta. To cikin ikon Allah yana fadi bai daina ba, sai ga shi bana Allah Ya nuna mana da idonmu ya samu nasara, shi ma sai da aka ce ya yi hawaye. Lokacin da na je yi masa murna (cin zaben fidda-gwani) sai na ce Janar to, alhamdulillahi, ina tsammani wannan karon za ka zama Shugaban kasa. Na ce wannan zaben da aka yi ya fi zabubbukan baya zama nagari. Ya ce saboda me? Na ce abokan hamayyarka akwai wadanda suka yi kaurin suna wajen cewa su suna da kudin da za su iya badawa ko nawa ne, su sayi mutane, kuma sun saba yin irin wannan kuma muna da labarin akwai wadanda suka sha alwashin yin haka. Kai kuma a fili ka ce ba ka da kudin da za ka ba mutane. Kuma ko kana da su ba wai ra’ayinka ba ne badawa, ka ce in za a zabe ka a zabi cancanta, kuma jama’a suka bi. Suka ki suka amshi kudin amma suka zabi cancanta. Na ce to tunda Allah Ya kawo mu yanzu har mutanen Najeriya sun koya, ka dade kamar kana yi musu wa’azi kana yi musu gargadi, amma a wannan karo ne suka yarda, na ce tunda wadannan mutane na Najeriya sun fi wahala, zaben ya fi wahala. Domin wakilan mutane ne da aka zaba suka karbi kudi suka ki suka zabe ka. To saboda haka, in Allah Ya yarda (zabe) na gaba daya ma in an zo shi ma za ka ci cikin sauki.
Aminiya: Ban san yaya kake ganin wannan ziyara da ya zo Daura, yana ban kwana da mutane zai je ya dauki wannan mukami, sai ka ce tamkar yana kara damara ne zai je yaki. Kana da wata fargaba cewa zai je yaki domin ka san ’yan Najeriya duk sun dauki burinsu sun dora kan shi wannan mutum daya. Kana ganin abu ne da zai iya kuma zai iya sauya abubuwan kamar yadda mutane ke tsammani?
Ciroma: Wato ba ni da wata fargaba a kan Janar Buhari a yadda na san shi. Balle Allah Ya ba shi Najeriya a lokacin da ta lalace, take nema ta wargaje, barna ta yi yawa a ciki, to in Allah Ya yarda na yarda Janar zai iya ba da ransa a kan Najeriya. Zai yi iyakacin kokarinsa sai an yi gyara, in ka ga sun bata da mutum to wanda ya ce ba za a yi gyara ba ne. Kuma ko fargaba ba ni da shi don na tabbata za a ci nasara, domin zai tsaya, ba zai so a sa masa baki ba, ko zaben wadanda za su taya shi aiki, ina jin sai ya yi dabara ya nemi wasu mutane da za su ba shi shawara kuma sai ya dubi halayen kowanne, ya ga irin abin da ya yi, ya ga irin tabargazar da ya yi. In mutum ya taba tabargaza ko aika-aika ba zai tafi da shi ba a yadda na sani. Shi mutum ne tsabtatacce Allah Ya tsabtace shi, to idan muka samu rikonsa shekara hudu in Allah Ya yarda za a mance dukkan wannan barnar da aka yi Najeriya za ta koma wata sabuwa daban, a iri tunanina. Za ta koma sabuwa daban yadda halayen mutane za su canja, tunda yanzu sun ki kudi, sun dauki cancanta saboda haka ashe idan ya zama Shugaban kasa wannan ra’ayi nasa na tsare gaskiya da amana ne zai fara fada a kan mutane. Domin tunda mun taba ganin lokacin da ya yi mulkin soja, yaki da rashin da’ar nan shi ma har ya kama ran mutane. Kowa ya gani a lokacin ko me ka dauka na datti ba ka son ka ajiye a kofar gidanka ko inda bai dace ba. Sai mutane su ce yaki da rashin da’a, har ya fara kama ran mutane, da ya dade da ba mu shiga cikin wannan hali ba.
Saboda haka gani nake yi an ce jiki magayi, an sha wahala iri-iri. Ba a abin da muke jin dadi a yanzu sai wadanda suka san wane ake yi da su wadanda suka cancanta ba a yi da su. Yanzu kuwa haka ba zai yiwu ba, domin duk wanda ya cancanta ko Musulmi ko Kirista ko marar addini matukar ka karanta abin da ake bukata za a yi da kai.
Da farko za a dan fuskanci wuya, saboda mutane sun saba da waccan hanya, amma in mutane suka saba za a gyara, abin da nake tunani mutane za su canja galibi su zama masu gaskiya, Najeriya za ta canja, amma za mu sha ’yar wahala kadan kafin ta canja, kamar karatu ne, in kowa ya riga ya fahimta cewa akidar nan ta Janar (Buhari) ita ce akida, domin Najeriyar kanta za ta canja. To bare mu mutanen Daura da ake fadi, mu mun dauka cewa kowa yana murna da Buhari a Najeriya ba mutanen Daura kadai ba.
Kuma mun tabbata ba zai ware mutanen Daura kadai ba, ba al’adarsa ba ce. Sai dai in abin da ake yi ya zo kan Daura ya yi, amma ba zai iya ware mu ya maida mu daban don yana Shugaban kasa ba. Zai ba mu hakkinmu akwai abubuwa da dama wadanda muka cancanta mu samu, amma ba zai fifita mu ba, na tabbata ba zai iya ware nasa ba, shi ba ya da son kai, yana da adalci, adalci kuma shi ne abin da Allah Ya ce a yi a cikin kowane addini ba sai Musulunci ba. In mutum zai yi adalci in ka ji haushinsa daga baya za ka gane, don za ka ga aikin adalci, za ka ga abubuwa sun canja. Matsala irin ta kasar nan, an ce Najeriya tana cikin kasashe masu arziki a duniya, amma talauci na damun mutanen kasar. Kuma in aka fada maka kudin da mutum daya ke da shi, sai mutum ya ji mamaki. To wannan hanya ka san masifa ce, ka dauki kudin mutane ka tafi wata kasa ka ajiye wanda iyakar rayuwarka wannan kudi lokacin da ka mutu sun kare. Da kyar ne ma in za su iya dawowa wajen iyalinka.
Wannan ai masifa ce, to wannan lokacin Buhari sai ka ga an bar wannan, in Allah Ya yarda. Kuma in aka samu laifi tabbatacce a kan mutum ko kan wasu kungiyoyin jama’a, wanda tabbatacce ne, ga shaida ga komai, to ka tabbata Buhari in dai hakkin jama’a ne sai ya hukunta su, ba zai canja ba, haka yake. Abin da ke da bambanci da mulkin soja ne, yanzu lokacin dimokuradiyya ne babu kama-karya. Na soja ko ana so ko ba a so za su ce kaza dole. To amma na san zai bi yadda tsarin mulki ya ce, ya tsare.
In dai a kan doka ne to wallahi zai tsare, ko mutane su ce suna so ko ba su so. Na tabbata ba zai yi abin da yake ba gaskiya ba ne, kuma babu wanda zai iya sanya shi ya yi abin da yake ba gaskiya ba ne. Saboda haka yanzu mu cikin farin ciki muke, a ce mutumin Daura ne ya zo ya gyara Najeriya, wannan abu in Allah Ya yarda in da ranmu za mu gani. In mun mutu wasu za su gani, in Allah Ya yarda kafin ya gama mulkinsa za a ga abin mamaki. Za ka ga mutane da kansu sun shiga taitayinsu, saboda ita gaskiya kowa ya san ta, amma sai a rika kware mata baya, mai gaskiya ba ya da farin jini, cikin magana ma sai a kwabe shi, ko in cikin aiki ne a cire shi. To wannan ba a lokacin Buhari ba, a lokacin Buhari in za a bincika a gano mutum da halinsa da akidarsa da irin karatun da ya yi da yadda amanarsa take, bai sani ba, bai yi komai ba a je a dauko shi a ba shi aiki ko mukami, wannan sai Buhari. Ba ruwansa wane ne mutum takardu yake aiki da su. In dan kasuwa ne sai ya ga wadanne irin ayyuka ya yi da can, kamfanin nasa wadanne irin ayyuka ya yi da can. In ya ga shaidar akwai gaskiya da inganci, to zai tafi da shi, idan kuma ya ga da wani lahani, to ba zai tafi da shi ba. To idan kuwa ana tacewa abu mai kyau yana da wahala, amma in an tabbata an gane shi, mutane da yawa za su taho a tafi. To shi ne muke ganin in Allah Ya yarda za mu yi alfahari musamman mu mutanen Daura. Zai ja mana a ce mutum ne mai amana, saboda shi kadai, dama ana cewa mutanen Daura mutane ne masu amana, to fitar Buhari za ta kara wanke mu. Mu a Daura ko da mutum yana jam’iyyar hamayya sai ya ce, eh, ni ina jam’iyyar hamayya, amma Buhari zan zaba, sai dan abin da ba za a rasa ba, tunda siyasa ce, amma galibinmu Buhari muka zaba.