Zamantakewar aure: Ko za mu dauki darasi daga labarin nan?
Gabatarwa: Ya ku masu bibiyar filin Sinadarin Kauna!Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa, ina yi muku albishir cewa a yau filin naku ya dawo, bayan bacewarsa na dogon lokaci. Muna ba ku hakuri tare da alwashin cewa in Allah Ya yarda za mu ci gaba da kawo muku dadadan bayanai da suka danganci soyayya da kauna. Muna […]
Gabatarwa:
Ya ku masu bibiyar filin Sinadarin Kauna!Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa, ina yi muku albishir cewa a yau filin naku ya dawo, bayan bacewarsa na dogon lokaci. Muna ba ku hakuri tare da alwashin cewa in Allah Ya yarda za mu ci gaba da kawo muku dadadan bayanai da suka danganci soyayya da kauna. Muna maraba da labarai, ra’ayoyi da tsokaci da suka danganci al’amuran soyayya da kauna. A yau za mu duba wani labari ne da ya danganci zamantakewar aure. Mun samu labarin nan ne daga marubuciya Umma Sulaiman ’Yan Awaki, Kano:
Wani magidanci ne da matarsa ta mutu ta bar shi da ’ya’ya hudu. Cikin ’ya’yan nan, babban namiji ne, ta biyu mace ce sai kuma maza biyu da ke bin bayanta.
A gidan haya suke don haka sai ya kara aure da nufin matar ta rika kula da marayun ’ya’yan nasa hudu. Ya auro bazawara wadda shi a ganinsa ita za ta fi kular masa da yaran maimakon ya auro budurwa.
Bayan kwana bakwai da auren nan sai matar ta fara fito da salo daban-daban, tana kulla wa yaran makirci a wurin babansu. Yau ta ce sun yi mata kaza, gobe ta ce an yi mata kaza. Wani lokacin kuma sai ta ki yin girki, ta hana su abinci, ta ce sun ki zuwa su yiwo mata cefane.
Haka baban nan nasu zai kama su ya yi ta jibga, sannan ya je ya sayo musu gasasshen nama ko tsire da burodi su ci shi da matar. ’Ya’yan kuwa sai dai su kwana haka da yunwa.
Kullum idan maigidan nan yana yi wa yaran nan nasa fada a kan matarsa, yakan rika furta cewa: “Wallahi, wallahi idan ba ku sani ba ku sani, a kan matata zan iya rabuwa da ku har abada!”
Ganin haka, sai wannan matar ta sake fito da wani sabon salon makirci. Ran nan maigidan ya dawo da dare sai ya samu matarsa ta hada kai da gwiwa tana ta rusa kuka, ga kuma kaya ta hada a gabanta na alamun shirin tafiya.
Cikin fargaba da zaro ido yake tambayarta inda za ta kuma me aka yi mata. Cikin kuka ta ba shi amsa cewa ta gaji da halin ’ya’yansa.
“Sai dai ka zabi daya, ko ni, ko kuma su amma wallahi ba zan zauna da su ba.” Abin da ta gaya masa ke nan cikin kukan munafunci da hawaye share-share.
“Wannan abu mai sauki ne.” Abin da ya ce mata ke nan tare da rarrashinta. Ba shi ya shawo kanta ta yi hakuri ba sai da gari ya waye.
Tunda safe ya fita daga gidan, wajen La’asar ya dawo da motar dibar kaya. Suka kwashe kayansu suka tafi suka bar yaran a gidan. Yaran da ba su da kowa sai mahaifinsu, mahaifiyarsu ta rasu kuma auro ta ya yi a wani gari.
Haka yaran nan suka zauna a gidan hayar nan, ba su da kowa, ba su da mai ba su abinci, ba su da mai tsawatar musu. Karatunsu ya tsaya saboda su suke fafutikar nemo abin da za su ci kullum.
Babban yaron shekararsa 17 kuma kullum shi ke bin kasuwanni yana daukar dako. Mai bi masa, mace ce ’yar shekara 15. Ita sai ta rika taya wata mata da suke haya gida daya aiki. Ita kuma matar in ta yi abinci sai ta rika diba mata. Kananan kuma maza biyu da dan shekara 12 da dan shekara 9, bakin hanya suke zuwa ana dora musu tallar ruwan leda.
Mai gidan hayar da suke zaune a gidanta da ta zo karbar kudinta ta ga halin da yaran suke ciki, dole ta tausaya musu ta ce su zauna sadaka.
Yanzu tsawon shekara biyu ke nan tunda mahaifin yaran nan ya tafi bai kuma waiwayarsu ba kuma yana nan a garin. Wani abin takaici ma shi ne, rayuwar budurwar ta fara canjawa, domin kuwa ta fara yin amfani da man bilicin, fatar jikinta duk ta fara kwalewa.
Abin tambaya a nan shi ne, shin ina yarinyar nan ta samu kudin yin shafe-shafe kuma wane ne ke yi mata jagorar yin haka?
Za ku iya aiko sakon tes a waya, WhatssApp ko I-mel:
08020968758