Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna […]

Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?
Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna da sassan al’umma daban-daban kuma ga abin da suka kalato daga bakunansu:

Mata ta fi kaunar mijinta
– Auwal Usman
Auwal Usman Goni: “Mace ta fi kaunar mijinta saboda su mata suna da tausayi sannan kuma duk wani abu na kulawa su suka fi bai wa miji fiye da yadda mijin zai bai wa matarsa. Yanzu da a ce miji zai kwanta jinya, matarsa za ta iya ta yi ta kula da shi har iya tsawon ransa ko har zuwa lokacin da zai samu sauki, amma shi mijin idan matarsa ce ta samu larura, zai iya yi mata kishiya. Idan mata ta samu wani abu na ci gaba, babu wanda zai fi cin moriyar abin kamar mijinta, sabanin mijin a kan matar tasa.”