Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?1

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna […]

Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?1
Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?1

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna da sassan al’umma daban-daban kuma ga abin da suka kalato daga bakunansu:

Mata mu muka fi kaunar mazajenmu
– Madam Jedidah

Jedidah Solomon: “Mu mata mu ne muka fi kauna da kulawa a kan mazajenmu da kuma nuna musu kauna. Ko wata dawainiya ta same mu, idan muna da hali ba mu fiye taimakon ’yan uwanmu kamar mazajenmu ba. Da a ce maza su ne suka fi kaunarmu a matsayin matayensu, da ko kishiya ba za su dinga yi mana ba, saboda yadda suke kaunar mu. Ko me kake yi wa namiji duk da haka ba ya gani, amma da yake mu Allah Ya yi mu da tausayi kuma muna karkashin ikonsu, shi ya sa ba yadda za mu yi, dole mu hakura da haka.”