Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?2
Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna […]
Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna da sassan al’umma daban-daban kuma ga abin da suka kalato daga bakunansu:
Mata ta fi son mijinta – A’isha Sani
A’isha Sani: “Ina ganin mace ta fi son mijinta, saboda son da take yi wa mijinta ko da wani abu zai same shi na canjin rayuwa misali ciwo, mace za ta zauna da mijinta a wannan hali, har sai abin da hali ya yi. Haka kuma saboda son da mace take yi wa mijinta takan yi hakuri da rashin wadatarsa, takan yi kokarin jalauta abin da ya kawo gidan komai kankantarsa. Haka kuma son da mace ke yi wa mijinta ke sa ta kare shi ko da a wurin iyayenta ne, ba za ta taba yarda a ga laifinsa ba.”