Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?3

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna […]

Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?3
Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?3

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna da sassan al’umma daban-daban kuma ga abin da suka kalato daga bakunansu:

Miji ya fi son matarsa – Garba Madaki
Garba Madaki: “Ni a ra’ayina, miji ya fi son matarsa, kasancewar tun farko shi ne ke fara furta so ga matarsa, kafin a je maganar aure. Idan an yi auren ma son matarsa ne yake ba miji kwarin gwiwar neman kudi, inda zai jure duk wata wahala don ya gamsar da matarsa ko kuma iyalinsa. Haka kuma son nan da namiji yake yi wa matarsa tun farko yake sanyawa ya kau da idonsa a kan duk wani abu da take yi masa na musgunawa.”