Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?4
Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna […]
Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna da sassan al’umma daban-daban kuma ga abin da suka kalato daga bakunansu:
Miji ya fi son mata – Muhammadu Kawure
Muhammadu Kawure: “Miji ya fi nuna so ga matarsa da nuna mata kauna domin miji shi yake nemo abincin da za ta ci kuma shi yake daukar dawainiyarta da lalurorinta saboda tsabar kaunar da yake yi mata. Shi ya sa ba za ka hada son da miji yake yi wa matarsa, ba ya kwatantuwa, idan aka yi la’akari da kasancewarsa maigida da Allah Ya dora masa nauyi.”