Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?5

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna […]

Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?5
Zamantakewar aure: Tsakanin miji da mata wa ya fi nuna so da kauna?5

Zamantakewar aure tana kasancewa ne tsakanin namiji da mace, wato tsakanin miji da mata. Haka kuma, abu ne da aka sani cewa soyayya na taka muhimmiyar rawa wajen samar da aminci tsakanin ma’aurata. Abin tambaya a nan shi ne, wai shin tsakanin miji da mata, wa ya fi nuna soyayya da kauna? Wakilanmu sun tattauna da sassan al’umma daban-daban kuma ga abin da suka kalato daga bakunansu:

Mata ta fi kaunar miji – Salaha Abdullah
Salaha Abdullah: “Mata ta fi nuna wa miji soyayya saboda duk lalurar da ta same shi ko ta rashin lafiya ko ta rashin abin duniya, mata tana iya daurewa ta ci gaba da zama da mijinta haka nan, saboda tsananin soyayya da kauna da tausayi da rikon amana, amma mazan aure na yanzu ba za su iya yin haka ba.”