An rufe kasuwanni 11 kan alaka da ’yan bindigar Zamfara

Zamfarawa na ganin hakan ba zai kawo karshen ayyukan ’yan bindiga ba

An rufe kasuwanni 11 kan alaka da ’yan bindigar Zamfara

Wnai yanki da Kasuwar Wuse da ke Abuja (Tsohuwar ajiya).

Gwamnatin Zamfara ta rufe kasuwanni guda 11 har sai abin da hali ya yi kan zargin ’yan bindiga na sayar da dabbobin sata a kasuwannin.

Kwamishinan tsaron jihar, Munnir Haidara, ya ce, “rufe kasuwannin yana da muhimmanci, saboda rahotannin da muka samu cewa ’yan bindiga na zuwa wadannan kasuwanni su sayar da dabbobin jama’a da suka sato.”

Haidara ya ce gwamnatin jihar a umarci jami’an tsaro su tabbatar da ana bin umarnin, tare da cafke duk wanda ya yi kunnen kashi.

Kasuwannin da aka rufe su ne kasuwannnin Tsafe da Bilbis a Karamar Hukumar Tsafe; Kasuwar Jangebe a Karamar Hukumar Talata-Mafara sai Kasuwar Wuya a Karamar Hukumar Anka.

Akwai kuma Kasuwar Magamin Diddi a Karamar Hukumar Maradun; Kasuwar Galadi a Karamar Hukumar Shinkafi; Kasuwar Mada a Karamar Hukumar Gusau.

A Karamar Hukumar Birnin Magaji kuma kawai da kasuwanin Sabon Birnin Danali, Kokiya, Chigama da Nasarawar Godel.

A zamanin tsohon gwamnan jihar kuma ministan tsaro a yanzu, Muhammad Bello Matawalle, ya rufe kasuwannin Mada, Danjinga, Maru, Maradun da Dansadau da dai saurnasu, a bisa a irin wannan dalili.

Sai dai wasu jama’ar jama’a sun soki matakin da cewa babu saukin da zai kawo, domin gwamnaocin baya ma sun rufe kasuwannini kan wannan dalilin amma bamu saukin da hakan samu.

Wani dan kasuwa, Alhaji Aminu Musa, ya shaida wa wakilimu cewa  “wannan ba zai kawo karshen ta’addanci a jihar ba, mu abin da muke shi shi ne gwamnati ta kawo karshen ta’addanci a jihar.

“A wannan hali na matsin tattalin arziki, babu abin da rufe kasuwannin zai yi illa kara jefa jam’aa cikin kunci. Karain jami’an tsaro ya kamata gwamnati ta girke a wuraren da ke fuskantar barzana daga ’yan bindiga.”

Shi ma Salihu Datti Tsafe, irin wannan ra’ayi gare shi domin kuwa, “mun gwammace zuwa kasuwa a kan zaman gida saboda matsalar tsaro.

“Wannan na nufin idan ma an yi garkuwa da ’yan uwanmu ba za mu samun abin da za mu biya kudin fansa ba.

“Gwamnati dai ya kamata ta sauya shawara domin wannan dai ba shi zai magance matsalar ’yan bindiga a Jihar Zamfara ba.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS