Zamfara ba zata ta rasa ‘yan takara a zaben 2019 ba- Yari
Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce, wajibi ne a abi wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta INEC wajen kammala zabukan fidda gwani na majalisar dokoki da ta jiha na jam’iyyar APC. A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Gusau, Gwamna Yari ya ce, jama’ar jihar su kwantar da hankulansu lokaci kadan za […]
Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce, wajibi ne a abi wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta INEC wajen kammala zabukan fidda gwani na majalisar dokoki da ta jiha na jam’iyyar APC.
A lokacin da yake ganawa da manema labarai a Gusau, Gwamna Yari ya ce, jama’ar jihar su kwantar da hankulansu lokaci kadan za a sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a jihar.
‘Yan takarar gwamnan jihar Zamfara wadanda suke kiran kansu rukunin G8 sun hada da: Mataimakin Gwamnan jihar Ibrahim Wakkala da Sanata Kabir Marafa, Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali da Aminu Sani Jaji, Injiniya Abu Magaji da Dauda Lawal da Mohammed Sagir Hamidu.