Zamfara: Matawalle ya kafa kwamitin mika mulki ga sabuwar gwamnati

Matawalle, wanda ya nemi tazarce a jam’iyyar APC, ya sha kaye a hannun Dauda Lawal na jam’iyyar adawa ta PDP

Zamfara: Matawalle ya kafa kwamitin mika mulki ga sabuwar gwamnati

Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle

Gwamnan Zamfara mai barin gado, Bello Muhammad Matawalle, ya kafa kwamitin mutum 41 domin tsare-tsaren mika mulki ga sabuwar gwamnatin jihar.

Matawalle, wanda ya nemi tazarce a jam’iyyar APC, ya kafa kwamitin ne bayan ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Dauda Lawal, a zaben ranar 18 ga watan Maris.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa aikin kwamitin shi ne tabbatar da mika gwamnati cikin tsari da kuma samar da bayanan da suka dace ga gwamnati mai jiran gado.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da gwamna mai jiran gado, Dauda Lawal, domin jagorantar Jihar Zamfara na tsawon shekara hudu.

Sanarwar da sakataran gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe, ya fitar ranar Alhamis ta ce tsohon ministan kudi, Bashir Yuguda ne zai jagoracin kwamitin.

Sakataren kwamitin kuma shi ne Dokta Lawal Hussain, Babban Sakataren Harkokin Majalisar Zartarwa a ofishin gwamna mai ci.