Zamfara ta rasa mutum 160 da shanu 6,000 ga ’yan fashi cikin wata uku – Yari
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari ya ce jihar ta rasa mutum 160 da shanu dubu shida da tumaki 400 ga ’yan fashi da makami cikin wata uku.A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamna Yari ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga Majalisar Dokokin Jihar kan halin da tattalin arziki da tsaro suke […]
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’aziz Yari ya ce jihar ta rasa mutum 160 da shanu dubu shida da tumaki 400 ga ’yan fashi da makami cikin wata uku.
A ranar Litinin da ta gabata ne Gwamna Yari ya bayyana haka lokacin da yake jawabi ga Majalisar Dokokin Jihar kan halin da tattalin arziki da tsaro suke ciki a jihar, inda ya ce ’yan fashin sun kuma sace mata goma a sassan jihar.
Ya ce, masu aikata wannan tu’annati sun bullo da sababbin dabaru na aikata miyagun ayyukansu. “Mun tunkari fadawa halin tawaye. Mu mutanen karkara ne, ba za mu iya barci hankalinmu a kwance ba, ko mu kame hannunwanmu mu kyale talakawa suna dandana kudarsu a hannun ’yan fashi ba. Shugaban kasa da ni ba mu da wani uzurin da za mu bayar kan rayukan da ake rasawa kusan kullum,” inji shi.
Gwamna Yari ya ce gwamnatin jihar tana tallafa wa jami’an tsaro da kudi da kayan aiki, inda ya ce idan da jihar za ta janye wannan tallafi miyagun ayyuka za su yi tashin gwauron zabo.
Ya ce, “Abin da yake faruwa a yanzu a yankunan karkararmu yana da matukar daga hankali da sanya damuwa kuma dole ne a kawo karshensa, idan muna son ci gaba. Wajibi ne a samu yunkuri da hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin tsaro domin a tabbatar da tsaron rayuka da dukiya.”
Sai ya yi kira kan a samu hadin kai a tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin samun nasara.