Zamfarawa kada ku yi sakaci a zabe mai zuwa – Bilbis
Tsohon Ministan Labarai Alhaji Ikira Aliyu Bilbis ya bukaci al’ummar Jihar zamfara da kada su sake su zabi Jam’iyyar PDP a zabubbuka masu zuwa matukar suna son ci gaban jihar da kasa baki daya. Toshon Ministan wanda shi ne Daraktan Yakin Neman Zaben Gwamna Abdul’aziz Yari a karo na biyu, ya bayyana hakan ne a […]
Tsohon Ministan Labarai Alhaji Ikira Aliyu Bilbis ya bukaci al’ummar Jihar zamfara da kada su sake su zabi Jam’iyyar PDP a zabubbuka masu zuwa matukar suna son ci gaban jihar da kasa baki daya.
Toshon Ministan wanda shi ne Daraktan Yakin Neman Zaben Gwamna Abdul’aziz Yari a karo na biyu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yawon kaddamar da kwamitin yakin sake zaben Gwamnan a kananan hukumomi 14 na jihar.
Alhaji Ikira ya ce bayan mawuyacin halin da Jam’iyyar PDP ta jefa kasar nan a ciki da kuma mawuyacin halin da ta jefa Jihar Zamfara a ciki, tare da yi mata bita da kulli, kan kudin aikin da Gwamnan Jihar ya yi na gina hanyoyin Gwamnantin Tarayya da Shugaban kasa da wasu magoya bayansa suka hana a biya jihar da gangan.
Ya ce ya dace al’ummar Jihar zamfara su yi duk abin da za su iya domin su kada PDP, inda tsohon Ministan ya sanya kofi a tsakanin kananan hukumomi cewa duk karamar hukumar da ta ba da mafi karancin kuri’a ga PDP za ta samu Naira miliyan daya.
Alhaji Bilbis ya ce a matsayinsa na tsohon dan Jam’iyyar PDP ya koma APC ne saboda halin kirki da Gwamnan Jihar Zamfara yake da shi irin na mai gidansa marigayi Shugaba ’Yar’aduwa, wanda hakan ya janyo ra’ayinsa ya ga ya dace ya fito ya taimaka masa don ciyar da jihar gaba.
Da yake karin haske ga mambobin kwamitin ya ce yana daga cikin aikinsu lallashin wadanda aka samu sabani da su, a bi su har gidajensu a ba su hakuri domin su zo a yi tafiya tare don cimma nasara.
Ya ja kunnen matasan jihar cewa canji ba zai yiwu ba sai an tanadi kuri’a don haka ya zama wajibi su yanki katin zabe, domin da shi ne za a yi canjin da ake bukata.