Zamfarawa sun yi artabu da ’yan bindiga har maboyarsu

Mahara sun bindige mutum 10 a harin da suka kai a Zamfara

Zamfarawa sun yi artabu da ’yan bindiga har maboyarsu

Mazauna wasu garuruwa a Jihar Zamfara sun yi ta maza inda suka bi ’yan bindiga har maboyarsu bayan ’yan bindigar sun kai musu hari.

Akalla mutum 10 ne aka kashe a harin da miyagun suka kai garurruwan Talle da Dutsingari da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Wani ganau ya ce, bayan ’yan bindigar sun far musu ne a ranar Litinin suna harbin jama’a ne daga baya ’yan garin suk yi ta maza suka bi su zuwa cikin dajin da suke zama.

“Kawai sun shigo gari ne suna ta harbi kan mai uwa da wabi.

“Mu ba mu da bindiga, amma sai muka dauki iya abin da muke da shi muka bi su cikin dajin domin kare kanmu amma suka ci gaba da harbin mutane.

“Sun kashe mana fiye da mutum 10, yanzu gawarwakin mutum bakwai na wurinmu sauran kuma sai mun shiga cikin daji mun dauko su,” kamar yadda ya shaida wa Sashen Hausa na BBC.

Mutumin ya kara da cewa daga baya sojoji sun isa garin, amma suka tafi ba tare da sun yi komai ba.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara, Abubakar Dauran ya tabbatar wa BBC samun rahoton harin wanda  ya ce daga bisani suka tura jami’an tsaro.

Ya ce Gwamnatin Jihar na jiran rahoton jami’an tsaro kan hakikanin abin da ya faru da kuma inda aka kwana.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya mafiya fama da matsalar ’yan fashin daji da kesatar dabbobi, garkuwa da mutane da kuma kisan ba gaira, ba dalili.

’Yan ta’addan sun yi wa mata fyade, sun kona garuruwa, baya ga sace dukiyar mutane da karbar kudaden fasa a kan mutanen da suka sace.

Ayyukan maharan ya tilasta wa dubban mutane gudun hijira da kuma hana su gudanar da harkokinsu na noma da wasu sana’o’i.

Duk da yunkurin gwamnatin jihar na yin sulhu da ’yan bindigar, har yanzu matsalar ba ta kawo karshe ba.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi